
Waɗanda ake zargin
Jami’an Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Nijeriya (NSCDC), sun cafke wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan kungiyar masu aikata laifuka ta yanar gizo ne, waɗanda suka ƙware wajen yin basaja a matsayin jami’an gwamnati a Facebook.
Yayin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a Abuja ranar Talata, Kwamandan Rundunar Babban Birnin Tarayya Abuja, Olusola Odumosu, ya ce waɗanda ake zargin sun buɗe wani shafin Facebook na bogi da sunan sa domin damfarar ‘yan Nijeriya kuɗaɗensu.
“Bayan gano wannan, na ba da umarni ga jami’an leƙen asiri da masu bincike da kuma sashin yaƙi da zamba da su bankaɗo waɗanda ke da hannu a shafin Facebook ɗin na bogi.
“A yau ne farautar da aka fara kimanin watanni bakwai da suka gabata, da kuma wani aiki na ɓoye da jami’ai na suka yi, tare da taimakon takwarorinmu na Jihar Delta da na Jihar Anambra, ya samu sakamako don masu shirya wannan aika-aika ta shafin Facebook na damfara suna hannunmu,” inji shi.
Ya bayyana sunayen waɗanda ake zargin sun haɗa da Henry Ushie Odep, namiji, ɗan shekara 34, daga Cross Rivers da Emanuel Ushie Odep, mai shekaru 23, ɗan Jihar Cross Rivers.
Ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin Emmanuel Ushie shi ne na farko da aka kama a Abuja, inji Odumosu, inda ya ƙara da cewa ya yi wani bayani mai amfani wanda ya kai ga kama Henry Ushie Odep, babban yayansa, wanda yake riƙe da wayar da ke ɗauke da shafin Facebook ɗin na bogi a lokacin da aka kama shi a Asaba, Jihar Delta.
“Emmanuel ya amsa cewa ɗan uwansa, Henry Ushie Odep, ‘ɗan Yahoo’ ne kuma shi ne ya ƙirƙiri shafin Facebook ɗin na bogi mai ɗauke da sunan Olusola Odumosu bayan an naɗa shi Babban Kwamandan Babban Birnin Tarayya Abuja a watan Agustan 2023.
Odumosu ya ce, “Ya amince da cewa shi ne wanda yake cire kuɗaɗen da ɗan’uwansa (Henry) ya aika zuwa asusun Opay ta na’urorin POS har sai da jami’an Rundunar Babban Birnin Tarayya Abuja suka kama shi.
A nasa ɓangaren, Henry ya ce ya fara zamba ta yanar gizo ne a shekarar 2016, kuma shi ne ya jawo ƙaninsa, (Emmanuel Ushie) cikin wannan damfara saboda yana damun shi kan kuɗaɗe.
Ya amsa laifin damfarar wasu maƙudan kuɗaɗe daban-daban na wasu ‘yan Nijeriya ta hanyar fakewa daban-daban a shafukan yana gizo.
“Bincike ya nuna cewa suna amfani da asusu na Opay, moniepoint da Palmpay don karɓar kuɗaɗe, amma ba su da asusun banki a bankunan kasuwanci na gargajiya.
“Sun kuma yi amfani da asusu guda biyu mallakar wani Victory Chinagorom, wanda a cewarsu bai taɓa sanin suna damfarar yanar gizo ba,” inji shugaban NSCDC.
A cewar Henry, abokinsa, Chibuike Okorie ne ya kawo shi cikin harkar. Chibuike ɗin yanzu haka yana ƙasar Kuwait saboda ya bar Nijeriya.
Rundunar ‘yan sandan ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin, inda ta ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin ne bisa dokokin da aka tanada bayan bincike.