Hukumar Ƙorafe-ƙorafen Jama’a da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta bayyana a ranar Juma’a a Kano cewa ya zuwa yanzu ta ƙwato naira miliyan 4.2 daga cikin naira miliyan 8 daga hannun mahukunta da ma’aikatan Gidan Talabijin na Abubakar Rimi (ARTV), Kano.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), ya ruwaito cewa, ARTV ta samu kwangilar tallata Darajar Abinci Mai Gina Jiki ta naira miliyan 93 daga ANRIN, wata ƙungiya mai zaman kanta (NGO).
Sai dai an raba kwangilar kashi biyu na kashi 50 cikin 100 na kuɗin kwangilar wanda ya kai naira miliyan 40.
NAN ta samu labarin cewa daga cikin jimillar kuɗaɗen, kashi 30 cikin 100 na kuɗin da aka biya, wanda ya nuna naira miliyan 12 an biya ne ga mahukuntan ARTV wanda wakilin kwangilolin ya samu kashi 10 cikin 100 wanda ya nuna naira miliyan hudu.
An kuma ruwaito cewa mahukuntan ARTV sun karɓa kashi 20 cikin 100, wanda ya nuna naira miliyan 8 na jimillar kuɗaɗen.
NAN ta kuma ruwaito cewa yanzu haka Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Kano ta ƙwato naira miliyan 4.2 daga hannun mahukuntan ARTV.
“Muna yin duk mai yiwuwa don ƙwato kashi 30 cikin 100 da suka karɓa daga kamfanin tallar; sannan kuma a gurfanar da su gaban kuliya.
“Mun yi mamakin rahotannin da wani sashe na kafafen yaɗa labarai suka bayar na cewa hukumar ta ba da shawarar a kori Manajan Darakta na ARTV da ma’aikatansa na gudanarwa.
“Hakan ba zai yiwu ba saboda har yanzu muna kan bincike kan lamarin. Babu lokacin da hukumar ta bayar da wannan shawarar,” majiyar ta shaida wa NAN.
A lokacin da aka tuntuɓi wani babban jami’in gudanarwa na kamfanin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce mahukuntan kamfanin na bayar da haɗin kai da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa domin magance matsalolin.