Back

Hukumar Yaƙi da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi na neman ma’aurata da mutane 4 ruwa a jallo kan safarar hodar iblis

A ƙarshen makon da ya gabata ne Hukumar Yaƙi da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta bayyana cewa tana neman wasu ma’aurata da wasu ‘yan ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi guda huɗu da suke safarar hodar Iblis daga Indiya zuwa Nijeriya.

Daraktan Yaɗa Labarai da Bayar da Shawarwari, Femi Babafemi, a wata sanarwa da ya fitar jiya Lahadi, ya ce an bayyana ma’auratan a matsayin Kazeem Omogoriola Owoalade (wanda aka fi sani da Abdul Qassim Adisa Balogun) da Rashidat Ayinke Owoalade (wacce aka fi sani da Bolarinwa Rashidat Ayinke), bayan kama wasu mambobin ƙungiyar huɗu a Legas inda aka ƙwato wata motar wasanni da wasu gidaje guda biyu nasu.

Ya bayyana cewa an kama mambobin ƙungiyar guda biyu; Imran Taofeek Olalekan da Ishola Isiaka Olalekan ne a ranar 3 ga Afrilu, 2024 a ƙoƙarinsu na fitar da hodar iblis mai nauyin kilogiram 3.40 a cikin jirgin Qatar da zai tafi ƙasar Oman ta filin jirgin sama na Murtala Muhammed, MMI, Ikeja, Legas.

“Yayin da Imran shi ne ma’aikacin da ke kai kayan ƙwaya zuwa ƙasar Oman, Ishola ya ɗauke shi aiki a matsayin shugaban ƙungiyar, wanda a yanzu bincike ya nuna a matsayin Alhaji Kazeem Omogoriola Owoalade, wanda takardar izinin zamansa ta Indiya take ɗauke da Abdul Qassim Adisa Balogun da ke Indiya.

“An yi nasara a ƙoƙarin wargaza ƙungiyarsa a Nijeriya bayan makonni biyar na sa ido da kuma bin diddigi lokacin da aka kama wani ɗan ƙungiyar, Hamed Abimbola Saheed, wanda ke aiki kai tsaye da shugaban ƙungiyar a ranar 14 ga Mayu, a unguwar Abule Egba da ke Legas.”

NDLEA ta ce, “Haƙiƙa Saheed ne ya ajiye Imran a otal kwana ɗaya kafin tafiyarsa zuwa ƙasar Oman sannan kuma ya ajiye shi da Ishola a filin jirgin saman Legas a ranar da aka kama su.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?