Back

Hukumar Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi ta kama mace mai ciki da bazawara

Jami’an Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) sun cafke wata motar bas ta kasuwanci dake ɗauke da kuɗi na jabu naira miliyan 3.2 da rahotanni suka bayyana mallakin wasu mutane uku ne: Favour Peter mai cikin wata takwas, mai shekaru 24; Esther Adukwu mai shekaru 27 da Ochigbo Michael mai shekaru 39.

Femi Babafemi, kakakin NDLEA ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, ranar Lahadi.

Ya ce an kama mutanen uku ne a tashar mota ta Jabi da ke Abuja a wani samame da aka yi a ranar Talata, 9 ga watan Afrilu, 2024, biyo bayan ƙwace takardar kuɗaɗen naira na bogi a Lokoja, Jihar Kogi.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da jami’an NDLEA tare da haɗin gwiwar rundunar sojojin ruwan Nijeriya da ke Lugard da ke Lokoja suka kama Aliyu Lawal mai shekaru 37 a kan hanyar Lokoja zuwa Abuja a ranar Litinin 8 ga watan Afrilu, inda suka ƙwato tabar wiwi 620 mai nauyin kilogiram 310 daga wajensa, yayin da jami’an NDLEA suka kama buhu 10 na sinadarin da ke sa maye mai nauyin kilo 98 a kan titin Okene-Lokoja-Abuja daga Jama Obodo, mai shekaru 44, a cikin wata motar bas da ta taso daga Ilesha a Jihar Osun ta hanyar zuwa Jihar Taraba a ranar Laraba 10 ga watan Afrilu.

A Jihar Kuros Riba, jami’an NDLEA sun kama wata bazawara da mijin ta ya rasu mai shekaru 40 da haihuwa kuma mahaifiyar ‘ya’ya biyu, Misis Theodora Ita a ranar Litinin 8 ga watan Afrilu a Bassey Edom a Calabar, bisa laifin haɗawa da siyar da wani sabon sinadari mai sa maye, NPS, da ake kira ‘Combine’ a gida, wanda shine cakuɗa nau’ikan cannabis daban-daban da opioids waɗanda aka jiƙa a cikin ɗanyen gin.

A lokacin da aka kama ta, an ƙwato lita 18 na sinadari mai hatsarin gaske a cikin gangunan fenti da aka yi amfani da su.

“A cikin sanarwar ta, ta yi iƙirarin cewa ta fara samar da miyagun ƙwayoyi da rarrabawa a watan Oktoba 2023,” inji Babafemi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?