Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) a ranar Talata ta lalata jimillar kilogiram 304,436 da kuma lita 40,042 na miyagun ƙwayoyi da aka kama daga sassan Jihohin Legas da Ogun.
Da yake magana kan lalata ƙwayoyin da aka kama a bainar jama’a a Ibereko da ke yankin Badagry a Jihar Legas, Shugaban Hukumar kuma Babban Jami’in hukumar, Birgadiya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), ya ce an lalata haramtattun ƙwayoyin da aka kama ne a fili biyo bayan umarnin kotu.
Ya yi kira ga jama’a da su ƙara tallafa wa ƙoƙarin da hukumar NDLEA da sauran masu ruwa da tsaki ke yi na daƙile illolin shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da safarar miyagun ƙwayoyi a Nijeriya.
Shugaban hukumar NDLEA ya bayyana cewa kayayyakin da aka lalata sun “haɗa da haramtattun ƙwayoyi masu tauri da na ruwa da kuma nau’o’in hodar iblis da tabar wiwi da tramadol da sauransu.”
Ya ce jami’an hukumar ta NDLEA a sassa daban-daban na hukumar ne suka kama su a Jihohin Legas da Ogun tun daga watan Janairun 2022 zuwa yau, musamman a tashoshin jiragen ruwa na Legas, da filayen jiragen sama, da kan iyakokin ƙasa.
“Za a lalata su a nan a yau bisa umarnin kotu, ƙwayoyi ne masu nauyin kilogiram 304,436.055 da lita 40,042.621 na ƙwayoyin ruwa.
“Lalata waɗannan kayayyakin ya dace da dokar NDLEA, wacce ta umurci hukumar ta lalata duk wani miyagun ƙwayoyi bayan an gurfanar da su a gaban kuliya. Muna so mu ce kasancewar ku a nan shaida ce ga wannan muhimmin aikin. Don haka, muna godiya ga duk masu ruwa da tsaki da jama’a da suka shaida wannan aikin,” inji shi.
Marwa ya bayyana jin daɗinsa ga sarakuna, shugabannin hukumomin tsaro, malaman addini, ƙungiyoyi masu zaman kansu da CSO da sauran masu ruwa da tsaki da suka halarci bikin.
“Zan yi amfani da wannan dama wajen amincewa da goyon bayan da abokan hulɗar hukumar na gida da waje ke bayarwa musamman Hukumar Yaƙi da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Amurka (US-DEA); NCA na Ƙasar Ingila; Jamusawa, Faransa; NCB ta ƙasar Indiya, da sauran waɗanda suka yi aiki da hukumar a kan wasu kame-kame, haka ma sojojin Nijeriya da sauran hukumomin tabbatar da doka da oda kamar Hukumar Kwatsam; Hukumar Shige da Fice; ‘Yan sanda; Jami’an Tsaron Farin Kaya; Hukumar Kiyaye Haɗurra; NFIU, NAFDAC da sauran su da suke taimaka wa ƙoƙarin mu na kawar da miyagun ƙwayoyi a Nijeriya.”