Back

Hukumar ‘Yan Sanda na son a hukunta CPs na Imo da Delta saboda sabbin kashe-kashen da aka yi a Delta

Shugaban PSC, Solomon Arase

Hukumar Kula da ‘Yan Sanda ta Ƙasa (PSC) ta buƙaci a sakawa Kwamishinonin ‘Yan Sanda a jihohin Imo da Delta takunkumi kan kashe wasu jami’an ‘yan sanda.

Hukumar ta ce musamman kashe-kashen da ake yi a wasu jihohin ya zama abin damuwa yayin da ta yi kira ga Babban Sufeton ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, da ya sake duba iyawar CPs a cikin dokokin jihar.

An ruwaito cewa aƙalla jami’an ‘yan sandan Nijeriya shida ne aka kashe a ‘yan kwanakin da suka gabata a wani harin kwantan ɓauna da aka kai a dajin Ohoro da ke ƙaramar hukumar Ughelli ta Arewa a jihar Delta, yayin da wasu jami’an ‘yan sanda 6 suka rasa rayukansu.

Hakazalika, a ranar Asabar ne wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ’yan Ƙungiyar Masu Fafutuka Kafa Ƙasar Biafra ne da kuma reshenta mai suna Eastern Security Network, suka kashe wasu ‘yan sanda biyu da ke aiki a MOPOL 18, Owerri, Jihar Imo.

Maharan sun yi ta harbin kan mai uwa da wabi ne a motar sintiri na ‘yan sanda da jami’an da suka mutun suke ciki a yankin Okigwe na jihar.

Da yake mayar da martani kan lamarin, Solomon Arase, shugaban hukumar ta PSC, a wata sanarwa ɗauke da sa hannun kakakin hukumar, Ikechukwu Ani, ya ce sanya wa kwamishinonin ‘yan sandan biyu takunkumi zai zama aya ga wasu da za a iya samu da gazawa nan gaba.

Ya yi Allah-wadai da sabon salon kashe-kashen da ake yi wa jami’an ‘yan sanda a bakin aiki, yana mai jaddada cewa su ma waɗannan jami’an ‘yan Nijeriya ne da suka cancanci goyon baya da ƙarfafa gwiwa da kuma ƙariya daga ‘yan ƙasa.

Arase, wanda shi ne IGP mai ritaya, ya jaddada cewa dole ne a samu sakamakon abin da ya bayyana a matsayin “hatsarin da za a iya kaucewa”, inda ya ƙara da cewa duk wani CP na jihar da aka samu bai cancanta ba, ya yi sakaci wajen yin aiki ko dabara, to ya kamata a sawwaƙe masa domin kauce wa irin waɗannan ɗimbin hasarar rayukan ‘yan sanda.

“Ina miƙa ta’aziyya ga Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Olukayode Egbetokun, kan wannan mummunan al’amari da ya faru musamman a daidai lokacin da ya kamata a haɗa hannu wajen kawar da ‘yan bindiga da ‘yan fashi da makami.

“Mun samu fiye da kaso mai tsoka na waɗannan munanan ci gaban a cikin ‘yan kwanakin nan. Don haka ina kira da a haɗa kai da jami’an leƙen asiri,” Ani ya ruwaito shugaban PSC yana cewa.

Shugaban na PSC ya kuma jajanta wa iyalan jami’an da aka kashe, inda ya ce lokaci ya yi da Kwamishinonin ‘Yan Sandan Jihohi za su tashi tsaye.

Ya kuma umurci jami’an da ke aiki da cewa kada su bari ci gaban da suke faruwa su rage musu karfin gwiwa, amma su sake aiwatar da kuzarin su na yaƙi wanda aka san rundunar da shi wajen kawar da sabbin hare-hare.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?