Back

Hukumar zabe ta kasa ta dakatar da sake gudanar da zabe a rumfunan zabe ashirin a jihohi uku.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta dakatar da sake gudanar da zabukan da ake yi a wasu mazabu saboda abin da ta bayyana a matsayin “rushewa, rashin bin ka’ida da kuma sace jami’an zabe”.

Kwamishinan yada labaran da wayar da kan masu zabe na kasa Sam Olumekun ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Abuja.

Yankunan da abin ya shafa dai su ne mazabar tarayya ta Ikono/Ini, jihar Akwa Ibom. Dakatar da zabe a rumfunan zabe guda biyu (Village Hall, EdemUrua 003 a Ini LGA da Village Hall Mbiabong Ikot Udo 003 a Ikono LGA) inda ‘yan daba suka kwashe duk kayan zaben.

ENUGU 

A Mazabar Jihar Enugu ta Kudu 1, an dakatar da zabuka a dukkan rumfunan zaben guda takwas inda ba a samu ainihin takardar sakamakon zaben da masu jefa kuri’a za su duba ba kafin a fara zaben.

KANO 

An Dakatar da Zaben Majalisar Jiha a Mazabar Kunchi da Tsanyawa a dukkan rumfunan zabe goma da ke karamar hukumar Kunchin saboda mamayewa, barna da kuma hargitsi na ‘yan daba”, in ji kwamishinan.

Olumekun ya ce matakin da hukumar ta dauka ya yi daidai da tanadin sashe na 24(3) na dokar zabe na alif dubu biyu da ashirin da biyu.

Yace, “Za a sanar da karin matakan da suka dace ga mazabun da abin ya shafa bayan taron Hukumar a ranar Litininmsi zuwa.

Ya kara da cewa, “INEC na gayyatar jami’an tsaro da su binciki lamarin, yayin da hukumar ta yi alkawarin yin bincike sosai kan duk wani sabani da ya shafi jami’anta”.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?