
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar da rahoton babban zaɓen shekarar da ta gabata.
Kwamishinan ta na Ƙasa kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Masu Kaɗa Ƙuri’a, Sam Olumekun ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
Wasu ‘yan Najeriyan sun bayyana rashin jin daɗin su kan jinkirin da aka yi na fitar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasan a shafin yanar gizo na hukumar.
Sai dai Olumekun ya ce an yi bitar rahoton zaɓen kuma an amince da buga shi a taron mako-mako da hukumar ta gudanar a ranar Alhamis.
Ya kuma bayyana cewa, an yi wannan wallafar ne bisa ga al’adar hukumar a zaɓuka huɗu da suka gabata, da kuma jajircewarta wajen tabbatar da gaskiya.
Olumekun ya ce “cikakkiyar takardar mai shafuka ɗari biyar da ashirin da shida, wacce aka tsara ta zuwa babi sha uku, aka kuma inganta ta da teburi sittin, da kwalaye sha huɗu, da kuma zane-zane goma, ta yi nazari mai zurfi kan muhimman tsare-tsare, nasarori, da ƙalubalen zaɓen, tare da muhimman darussa da aka koya.”
Da yake ƙarin haske, kwamishinan na ƙasa ya bayyana cewa “Rahoton ya nuna yadda zaɓen ya nuna bambamci da ba a taɓa ganin irinsa ba a cikin wakilcin jam’iyya, wanda ke nuna gagarumin ci gaban dimokradiyya.
“Wannan zaɓen ya ga jam’iyyun siyasa huɗu sun lashe zaɓen gwamna, jam’iyyu bakwai sun lashe kujerun majalisar dattawa, takwas a mazaɓar tarayya, da tara a majalisun jihohi, wanda hakan ke nuna gagarumin sauyi na wakilcin siyasa a faɗin Najeriya.
“Rahoton ya jaddada muhimmiyar rawar da ci gaban fasaha ke takawa, musamman Na’urar Tantance Masu Kaɗa Ƙuri’a (BVAS), wajen inganta gaskiyar zaɓe da rage maguɗi.
“Bugu da ƙari, ya yi magana akan damuwar jama’a game da shafin yanar gizo na duba sakamako na INEC, tare da bayyana matsalolin fasaha da aka fuskanta yayin ƙaddamar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.”
Ya ƙara da cewa sauran abubuwan da rahoton ya ƙunsa sun haɗa da safaran kayayyakin aiki, tsare-tsare na tsaro, dauƙan ma’aikata da horarwa, matakan haɗa kai, da tsarin zaɓe,” inji shi.
Olumekun ya ci gaba da bayyana cewa hukumar za ta yi maraba da shawarwari don sauye-sauye da inganta zaɓe nan gaba.