Back

Hukumomin NITDA, SMEDAN za su gina wa masu ƙanana da matsakaitan sana’o’i ma’ajiyar bayanai

Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA) da Hukumar Bunƙasa Ƙanana da Matsakaitan Sana’o’i ta Ƙasa (SMEDAN) sun amince da gina ma’ajiyar bayanai domin bunƙasa kasuwancin ƙanana da matsakaitan sana’o’i sama da arba’in.

Hukumomin biyu sun ce haɗin gwiwar za ta kare ayyuka miliyan saba’in a dukkan ɓangarori da kuma kiyaye kaso hamsin cikin ɗari na gudunmawar da za su bayar ga ɗaukacin darajan kayayyakin da aka samar (GDP) na ƙasar.

Darakta-Janar na NITDA, Kashifu Inuwa ya ce hukumomin za su haɗa kai don samar da shirye-shiryen haɗin gwiwa ta fuskar ababen more rayuwa, ilmin yanar gizo gizo, da dai sauransu.

Inuwa ya bayyana haka ne a wani taro da Darakta-Janar na SMEDAN, Mista Charles Odii a hedikwatar NITDA da ke Abuja.

A cewar wata sanarwa daga Shugabar Harkokin Sadarwa na NITDA, Hadiza Umar,  taron ya amince da haɗin gwiwa ta fuskar samar da ababen more rayuwa da ci gaban jarin ɗan Adam ga Ƙanana da Matsakaitan Sana’o’i (SME).

Inuwa ya bayyana cewa akwai damammaki na haɗin gwiwa tsakanin NITDA da SMEDAN kamar yadda ya bayyana a cikin Dabaru da Tsarin Aiki na NITDA, inda ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a sanya hannu kan Yarjejeniyar Fahimtar Juna (MoU) don fara shirye-shiryen.

Ya ce haɗin gwiwar zai sauƙaƙe samar da ilimin yanar gizo gizo a tsakanin Ƙanana da Matsakaitan Sana’o’i (SMEs) don haɓaka aiki.

Ya ƙara da cewa ya kuma yi daidai da manufar Tsarin Ilimin Yanar Gizo Gizo na Ƙasa (NDLF).

“Dukkanmu mun san cewa da ilimin yanar gizo gizo mace mai kasuwanci za ta iya sayar da kayanta ba tare da yin motsi daga wannan wuri zuwa wani ba, saboda wani yana iya amfani da kafa na yanar gizo gizo don yin odar kayayyaki kuma a kai musu.”

Darakta-Janar na NITDA ya bayyana cewa haɗin gwiwar ya dace domin zai ƙarfafa aiwatar da manufofi da kuma tsare-tsaren doka kamar Dokar Fara Sana’a ta Najeriya.

Ya ce SMEs na da kusan kashi tamanin cikin ɗari na ma’aikatan ƙasar da kuma sama da kashi tamanin na ‘yan kasuwa, inda ya jaddada cewa “Muna son yin aiki tare da ku, don gano yadda za mu sa SMEs su ci gajiyar duk wani abin ƙarfafa gwiwa a cikin Dokar Fara Sana’a kuma muna hanƙoran waɗanda ke amfani da ƙirƙira don haɓaka aiki ko masana’antu masu ƙirƙira.”

Mista Odii a cikin jawabinsa ya ce Hukumarsa na da wasu shirye-shirye na ilimin yanar gizo gizo da suka fara, inda ya bayyana cewa sun kasance a NITDA don ƙarin haɗin gwiwa kuma sun samu damar yin amfani da manhajar NITDA don tabbatar da cewa ƙoƙarinsu ya dace da ƙa’idojin duniya.

“Mun fahimci cewa NITDA ita ce sakateriyar dokar fara sana’a, kuma muna so mu yi aiki tare da ku wajen wayar da kan SMEs, musamman waɗanda suke farawa don cin gajiyar wannan.

“Muna da ingantacce ma’ajiyar bayanai na SME wanda muke ginawa, kuma muna son yin haɗin gwiwa tare da ku don tabbatar da cewa tsarin wannan ma’ajiyar bayanan ya yi daidai da abin da kuke da shi.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?