Masu fafutukar neman kafa kasar Biafra sun bukaci al’ummar yankin Kudu maso Gabas da kada su shiga zanga-zangar da ‘yan Najeriya ke yi na nuna adawa da halin kuncin da kasar ke ciki a karkashin gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
Kungiyar ‘yan awaren ta yi gargadin cewa bai kamata a yi irin wannan zanga-zangar ba a jihohin Kudu maso Gabas domin Igbo sun dade ba su da sha’awar zama da Najeriya kuma suna jiran damar ficewa ne kawai.
Kungiyar ta yi wannan ikirarin ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata ta hannun mai magana da yawunta, Emma Powerful.
Powerful ya yi gargadin cewa duk wanda ya shirya wata zanga-zangar adawa kan matsalar tattalin arziki a yankin Kudu maso Gabas zai jefa Ndigbo cikin hadari.
A baya-bayan nan dai kasar ta sha fama da tashe-tashen hankula da zanga-zanga kan tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayan abinci.
Sai dai kungiyar koli ta al’adun kabilar Igbo, Ohanaeze Ndigbo, a ranar Litinin, ta yi kira ga ‘yan kabilar Igbo da kada su shiga irin wannan zanga-zangar nuna adawa ga gwamnatin tarayya wadda Tinubu ke jagoranta.
Ƙungiyar Ohanaeze ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi hakuri da Tinubu.
Powerful ya ce, “Ya kamata a ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya su kasance abin damuwa ne ga ‘yan Nijeriya, ba wai ‘yan Biafra ba. ‘Yan Biafra ba su da sha’awar al’amuran Najeriya. An ci zarafin masu fafutukar kafa kasar Biafra, an yi musu barazana, an yi musu dukan tsiya, an kashe su da kuma hana su hakkin zabe a lokacin zaben wannan gwamnati mai ci. An gaya wa Ndigbo su jira, cewa ba lokacinsu ba ne su yi mulki.”
“A yayin zanga-zanga ta #EndSARS, Gwamnatin Tarayya ta zargi Ndigbo da yunkurin lalata Najeriya da tashin hankali. Ba ma son irin wannan bayanin da niyyar maimaita kan shi ta hanyar shigar Ndigbo wata zanga-zangar Najeriya.”
“Ya kamata Ndigbo su bar wahalhalun da tattalin arzikin kasar ke ciki, a halin da ake ciki ga ƙasar da ake kira Najeriya domin ‘yan Nijeriya su yi maganin su, domin wannan wahalar ita ce abin da Allah Madaukakin Sarki ya tanada wa Nijeriya kan laifukan da suka aikata a kan ‘yan Biafra a tsakanin shekarar 1967 zuwa ta 1970 zuwa yau.”
“Mun fahimci cewa Ndigbo suna fama da matsalolin tattalin arziki da suka taso daga tsare-tsaren tattalin arziki na gwamnati na rashin hankali, amma har yanzu Allah yana ganin Biafra. Mun damu da wahalar da wasu ƙabilu suke yi, amma babu abin da za mu iya yi. Halin da ake ciki a yanzu shi ya sa ‘yan Biafra ke fafutukar neman ‘yanci. Amma duk da haka, dole ne mu yi amfani da hikima.”
Kungiyar ta ci gaba da cewa duk wani ko wata kungiyar da ke son shirya zanga-zangar domin wahalar da ‘yan Najeriya ke ciki, to ya kamata ya je yankin arewacin ƙasar, ko yammacin kasar ya yi irin wannan zanga-zangar a can.”
“Yankin mu na fama da matsalar rashin tsaro da garkuwa da mutane da kuma kashe-kashen da hukumomi da jami’an gwamnatin tarayya ke yi, ciki har da ‘yan ta’adda. Muna da abubuwa da yawa a hannun mu da za mu yi. Ba za mu ƙyale kowa ko wata ƙungiya ta yi amfani da tsarin zanga-zangar don shigo da ƙarin jami’an tabarbarewar zaman lafiya cikin yankinmu ba,” inji shi.