
Gwamna Uba Sani da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu
Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya ce a kullum yana magana da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu sau biyu kan matsalar tsaro a jihar.
Uba Sani ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi.
A ranar 8 ga watan Maris ne wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki makarantar firamare da ƙaramar sakandare ta LEA da ke Kuriga a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna inda suka yi awon gaba da ɗalibai aƙalla 312 da wani shugaban makarantar, Abubakar Isah, da rana.
A daren Lahadi ne kuma ‘yan bindiga suka yi garkuwa da aƙalla mutane 86 a ƙauyukan Tantatu da Aguba da ke gundumar Kufana a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.
Sai dai a yayin hirar, gwamnan ya bayyana cewa Tinubu da hafsoshin tsaro sun duƙufa wajen kawo ƙarshen rashin tsaro a Nijeriya.
Ya ce, “Shugaban Ƙasa ya damu sosai. Ina magana da Shugaban Ƙasa sau biyu kowace rana kan wannan batu kuma ya nuna damuwa sosai. Ya jajirce kuma na yi imani da abin da Shugaban Ƙasa yake yi. Na kuma yi imani da sojojin. Ba na shakka a raina cewa za mu shawo kan wannan matsalar.
“Mun yi taro da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro na Ƙasa da shugabannin ma’aikata kuma kowa ya damu. Shi ma Shugaban Ƙasa ya damu. Yakan kira ni sau biyu a kullum, wani lokacin sau huɗu a rana, domin ya tambaye ni halin da jihar ta ke ciki. Ba ni da tantama a raina cewa Shugaban Ƙasa ƙarƙashin ingantacciyar shugabancinsa zai magance wannan matsala. Al’amari ne na lokaci.”
Uba Sani ya ƙara da cewa gwamnatin sa ta ɓullo da wani shiri domin taimakawa al’ummar jihar ta hanyar ƙarfafa kasuwanci da gidaje.