Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta yi watsi da babban taron jam’iyyar Labour (LP) da aka yi a Anambra.
Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Shugaban INEC, Mista Rotimi Oyekanmi, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a Abuja ranar Alhamis.
Oyekanmi ya ce INEC ba ta sanya ido a kan yadda taron ya gudana ba, inda ya ƙi bayyana dalilin da ya sa ba a sanya ido a kai ba.
Sai dai NAN ta ruwaito cewa a ranar Talata ne jam’iyyar LP ta sauya wurin babban taron daga Umuahia a Abia zuwa Nnewi, jihar Anambra.
Da yake magana kan sauya wurin taron, Mista Kehinde Edun, Mashawarcin LP na Ƙasa kan Harkokin Shari’a, ya shaida wa manema labarai cewa, jam’iyyar ta sanar da INEC yadda ya dace game da canjin wurin da rana.
“A’a, ana gudanar da shi a Anambra. Nnewi, a zahiri, ba Umuahia ba a jihar Abia. Hasali ma, Umuahia ba ita ce wurin farko da muka zaɓa ba. Benin ce ta farko kafin mu canza zuwa Umuahia, yanzu kuma Nnewi.
“Don haka, muna da ‘yancin zaɓar kowane wurin da muka zaɓa. Ana buƙatar mu sanar da INEC game da canjin wuri da lokaci ne kawai,” inji Edun.
Sashe na 82 (1) na Dokar Zaɓe, 2022, ya ce jam’iyyun siyasa za su baiwa INEC sanarwar aƙalla kwanaki 21 na babban taro ko wani taro.
Wannan ya haɗa da babban taro ko taron da aka yi don “haɗewar jam’iyyu” da zaɓen mambobin kwamitocin zartarwar su da sauran hukumomin su ko zaɓen ‘yan takara.