A ranar Lahadi ne Isra’ila ta janye sojojinta daga kudancin Gaza, ciki har da birnin Khan Yunus, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na soji da na Isra’ila suka bayyana, bayan shafe tsawon watanni ana gwabza ƙazamin faɗa da mayaƙan Hamas a yankin.
Amma sojojin, da aka fi sani da IDF, sun ce “muhimmiyar runduna” za ta ci gaba da aiki a sauran yankunan Zirin Gaza da aka yi wa kawanya.
“Rundunar kwamando ta 98 ta kammala aikin ta a Khan Yunis,” inji rundunar a wata sanarwa da ta aikawa kamfanin dillancin labarai na AFP. “Sashen dakarun ya bar zirin Gaza domin jinya da kuma shirya gudanar da ayyuka a nan gaba.
Sanarwar ta ce, “Muhimmiyar runduna da sashen dakarun 162 da na Nahal ke jagoranta na ci gaba da gudanar da ayyukansu a zirin Gaza kuma za su kiyaye ‘yancin yin aiki na rundunar ta IDF da kuma ikonta na gudanar da sahihin ayyukan sirri.”
Jaridar Haaretz ta Isra’ila ta ce janyewar ta dabara ce.
Wani jami’in soja ya gaya wa jaridar cewa “babu buƙatar mu ci gaba da kasancewa a sashin ba tare da buƙatar [aiki] ba”.
“Sashen dakaru na 98 ya tarwatsa rundunan Khan Yunis ta Hamas tare da kashe dubban mambobinta. Mun yi duk abin da za mu iya a can.”
Jami’in ya bayyana cewa, Falasɗinawa da suka rasa matsugunansu daga Khan Yunis na iya komawa gidajensu bayan da suka fake a birnin Rafah da ke kudancin ƙasar.
Amma, sojojin “za su ci gaba da aiki a can bisa ga buƙatun aiki,” inji jami’in.
Birnin da a da akwai yawan jama’a, Khan Yunis ya kasance wurin da aka kwashe watanni ana gwabza ƙazamin faɗa, inda aka kai hare-haren bama-bamai ba tare da kakkautawa ba.
Duk da ƙorafin da ƙasashen duniya suka yi, gwamnatin Isra’ila ta sha alwashin kai farmaki ta ƙasa a birnin Rafah da ke maƙwabtaka da ita inda sama da ‘yan Gaza miliyan ɗaya da rabi suka nemi mafaka.
Yaƙin Gaza ya samo asali ne sakamakon harin da ƙungiyar Hamas ta kai a ranar 7 ga Oktoba, 2023, wanda ya yi sanadin mutuwar ‘yan Isra’ila da baƙi 1,170, waɗanda akasarinsu fararen hula ne, a cewar wani alƙaluman da kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayar bisa alƙaluman hukuma na Isra’ila.
Aƙalla mutane 33,175 ne aka kashe a yankin Falasɗinawa a yaƙin neman ramuwar gayya na Isra’ila, a cewar ma’aikatar lafiya ta Hamas ta Gaza.