Back

Iyalai Dubu Saba’in Sun Ci Moriyar Kayayyakin Abinci Na Naira Miliyan 225 Daga Gwamnan Borno

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum,  ya raba kayayyakin abinci da kuɗinsu ya kai Naira miliyan dari biyu da ashirn da biyar ga iyalai sama da mutum dubu saba’in  da ke karamar hukumar Bama a Jihar.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, a ranar Litinin ɗin da ta gabata ya raba kayan abinci da kuɗin su ya kai Naira miliyan dubu ashirin da biyar ga iyalai masu rauni fiye da mutum dubu saba’in a ƙaramar hukumar Bama ta jihar.

An raba kayan abincin ne a lokacin da gwamnan ya ziyarci yankin domin jan hankalin jami’an tsaro kan hanyar da ta dace a inganta zaman lafiya a yankin.

Ya ce anyi rabon kayan abinci da tsabar kuɗin ne domin a taimakawa al’ummomin da ‘yan tada ƙayar baya suka addaba domin kuma gwamnatin ta dakile tunanin wasu zama ‘yan Boko Haram.

“Wannan yana daga cikin ci gaba da ƙoƙarin da muke yi ne na bayar da taimako ga marasa galihu a Bama waɗanda rikicin Boko Haram ya shafa masu ƙarancin rufin asiri,” in ji Zulum.

Mata dubu arb’a’in da biyar ne suka samu tsabar kuɗi biyar-biyar, kowacce  da zani turmi ɗaya, yayin da kowane magidanci ya karbi naira dubu ashirin da biyar da buhun shinkafa da masara.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?