Back

Iyali sun zargi jami’in soja a Kano da kashe ɗansu, sun buƙaci a yi hukunci

Marigayi Yusuf Shu’aibu

Al’ummar unguwar Gwagwarwa da ke ƙaramar hukumar Nassarawa a Jihar Kano na neman a yi musu shari’a kan zargin kashe wani matashi mai suna Yusuf Shu’aibu mai shekaru 23 da haihuwa da wani jami’in soja ya yi.

An bayyana cewa wani jami’in soja mai suna Oga Aminu ne ya ji wa marigayin wanda ke aiki a matsayin mai aikin tsafta a Asibitin Sojojin Saman Nijeriya da ke Kano, munanan raunuka.

Shu’aibu Bala, mahaifin marigayin ne ya ba da labarin abin da ya faru.

Ya ce, “Bayan ya kammala aikin dare, Yusuf yana shirin komawa gida sai Oga Aminu ya umarce shi da ya yi wani aiki. Bayan kammala aikin, Yusuf ya nemi a ba shi kuɗin abinci, amma a maimakon haka, ya fuskanci mummunan hari, wanda ya bar masa alamun cizo a jikinsa.”

Ya roƙi Gwamna Abba Kabir Yusuf, Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, Hukumar Kare Haƙƙoƙin Dan Adam ta Ƙasa, da Hafsan Hafsoshin Sojan Sama, Air Marshal Hassan Abubakar, da su tabbatar iyalin sun samu adalci.

Daraktan Hulɗa da Jama’a da Yaɗa Labarai na NAF, Air Vice Marshal Edward Gabkwet, ya bayyana cewa, Hafsan Hafsoshin Sojin Sama, Hassan Abubakar, ya bayar da umarnin gudanar da bincike.

A cewar Gabkwet, marigayin ya samu saɓani ne da wani sojan sama a kwanakin baya, wanda da alama an sasanta. Duk da haka, ba a san yanayin da ke tattare da rasuwar Yusuf ba.

Gabkwet ya ce NAF ta himmatu wajen bankaɗo gaskiyar rasuwar Shuaibu tare da miƙa ta’aziyya ga iyalansa.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?