Back

Iyayen yara miliyan 20 da ba su zuwa makaranta suna fuskantar haɗarin shiga gidan yari

Cikin damuwa da yawan yara miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya, Majalisar Dattawa a ranar Laraba ta yi kira da a kafa kotunan tafi-da-gidanka don tabbatar da Dokar Ilimi ta Duniya.

Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, ya buƙaci jihohin tarayya da na Babban Birnin Tarayya, da su ɗauki matakan da aka yi amfani da su a jihar Akwa Ibom lokacin da yake gwamna, wanda ya haɗa da ɗaurin watanni shida a gidan yari ga iyaye ko masu kula da yaran da suka isa zuwa makaranta da ake samunsu akan tituna ko a gona, a lokutan makaranta.

Yunƙurin da Majalisar Dattawa ta yi na ɗaukar tsauraran matakai kan iyaye ko masu kula da yaran da ba su zuwa makaranta a Nijeriya ya biyo bayan wani ƙudiri da Sanata Idiat Oluranti Adebule (APC Legas ta Yamma) ta ɗauki nauyi kan yara miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya.

Sanata Idiat a cikin ƙudirin ta ce abin damuwa ne, duba da rahoton 2022 na Hukumar Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO), cewa kimanin yara miliyan 20 na Nijeriya ba sa zuwa makaranta wanda ke wakiltar kashi 10 daga cikin al’ummar Nijeriya miliyan 200 da aka ƙiyasta kuma yana wakiltar mafi yawan adadin yaran da ba sa makaranta daga kowace ƙasa a duniya.

“Duk da cewa Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta yi saɓani kan wannan adadi, amma an yarda cewa ko mene ne ainihin alƙaluman, batun yaran da ba su zuwa makaranta ya zama wani cikas ga Nijeriya wanda dole ne a magance shi cikin gaggawa,” inji ta.

A nasa gudunmuwar, Sanata Adams Oshiomhole (APC Edo ta Arewa), ya ce dole ne a magance matsalar cikin gaggawa domin jahilci yana haifar da fatara, fatara kuma yana haifar da aikata laifuka.

“A gaskiya ba na jin muna buƙatar wani koyarwa don tunatar da mu cewa wanda bai samu dama ba ko kuma aka hana shi damar zuwa makaranta, an ƙaddara shi ya zama talaka har abada.

“Saurayi ko budurwar da ba sa iya karatu za su haifi yaron da bai iya karatu ba wanda zai haifar da daular talakawa wanda zai zama haɗari ga masu hannu da shuni da sauran al’umma baki ɗaya.

“A yau a Nijeriya, muna iya gani kuma dukkanmu shaida ne cewa rashin daidaito tsakanin mutane da matsanancin talauci a ko’ina ya haifar da babbar barazana ga tsaro ga kowa a Nijeriya. A bayyane yake cewa duka yaran Nijeriya na buƙatar zuwa makaranta,” inji shi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?