
Rundunar ƴan sanda ta Zone 2, Onikan, jihar Legas ta ce jami’an ƴan sandan uku da suka buƙaci masu ababen hawa da su ba su takardar izinin baƙin gilashi na fuskantar shari’a bisa samunsu da laifin rashin da’a.
Jami’ar Hulɗa da Jama’a na Shiyya, SP. Tunni Ayuba, ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa ranar Laraba a Legas.
Ta bayyana jami’an masu laifi, ASP Kenedy Ereoah, Insp. Ademiluyi Adekunle da Insp. Ayo Gbenga.
Ayuba ta ce mutanen ba masu garkuwa da mutane ba ne, amma jami’an da ke aiki da rundunar shiyya ta Zone 2 ne.
“An jawo hankalin ƴan sanda a shiyyar Zone 2 ga wani faifan bidiyo da mai amfani da ‘X’ ya saka mai suna @EmmCee_RNB a ranar 25 ga watan Janairu, inda wasu mutane uku da ke da’awar ƴan sandan da ke aiki da rundunar suka buƙaci a ba su takardar izinin baƙin gilashi daga direban mota.
“An mayar da martani ga tweet ɗin, yayin da aka fara bincike kan sunayen jami’an.
“Mutane ukun dukkansu suna aiki ne a Ofishin Leken Asiri na Shiyya, hedkwatar shiyya ta 2, Onikan, Legas.
“Saɓanin da’awar cewa su masu garkuwa da mutane ne, suna bakin aiki ne amma suka yi rashin ɗa’a.
“Jami’an sun yi laifi kuma a halin yanzu ana shari’arsu saboda saɓa wa umarnin Sufeto-Janar na ƴan sanda kan izinin gilashi,” in ji ta.
Ayuba ta buƙaci direban motar da abin ya shafa da ya tuntuɓe ta domin ɗaukar mataki.
“Domin a bayyana gaskiya, rundunar tana so ta buƙaci jama’ar da abin ya shafa su tuntuɓi ZPPRO ta hanyar GSM Lamba 08100025614 domin ɗaukar mataki,” inji ta.
A cewarta, Mataimakin Sufeto Janar na ƴan sandan ya yi kira da a kwantar da hankula tare da tabbatar wa mazauna jihar Legas da Ogun kan tsaron rayuka da dukiyoyin su yayin da suke gudanar da sana’o’insu na halal. (NAN)