Back

Jagorancin ƙwarai na da muhimmanci ga ayyukan sojoji

Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, a wajen taron

Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya bayyana cewa nagartaccen jagoranci yana da matuƙar muhimmanci ga ayyukan soji wajen yanke shawara a dukkan matakai.

Ya ƙara da cewa yana da muhimmanci wajen tafiyar da al’amura masu sarƙaƙiya da kuma tabbatar da haɗin kai wajen aiwatar da dabarun soji.

Wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar Da Kai, Henshaw Ogubike, ya fitar a ranar Laraba, ta ce ministan ya bayyana hakan a yayin taron ƙara wa juna sani na Kwas na 46 na manyan sojoji kan Yaƙar Ta’addanci a Nijeriya (CTCOIN) na 2024 a Kwalejin Rundunoni da Ma’aikatan Sojoji da ke Jaji a Jihar Kaduna.

Yayin da yake jawabi a matsayin babban baƙo na musamman a taron, ministan ya jaddada tasirin jagoranci a kan jami’ai kuma ya buƙaci mahalarta taron da su nuna ƙwazo da ƙwarewa wajen gudanar da ayyukan su.

Yayin da yake bayyana ƙalubalen da ke tattare da ayyukan ta’addanci, ministan ya yaba da ƙwazo da sadaukarwar da rundunar sojojin ƙasar nan suke yi wajen tabbatar da tsaron ƙasa, inda ya jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya na murƙushe ‘yan ta’adda ta hanyar samar da ingantaccen tsarin tsaro da haɗin gwiwar al’umma.

Badaru ya yi kira da a samar da cikakken tsarin gwamnati wajen magance ayyukan ta’addanci da ‘yan bindiga, yana mai jaddada muhimmancin gudanar da ayyukan leƙen asiri da kuma kare al’umma.

Ministan ya bayyana muhimmancin ƙarfafa haɗin gwiwa tare da al’ummomin cikin gida, abokan hulɗar ƙasa da ƙasa, da sauran hukumomin tsaro don inganta ayyukan tsaro, tare da nuna muhimmancin haɗin gwiwa wajen ayyuka da amfani da sababbin fasahohi a dabarun soja na zamani.

Saboda haka, ya nuna jin daɗin sa da yunƙurin gudanar da ayyukan haɗin gwiwa da Hafsoshin Soja na yanzu suke yi.

Ministan ya kuma jaddada muhimmancin kiyaye ƙa’idoji da muhimman ɗabi’u a cikin sojoji, yana mai jaddada buƙatar tsare gaskiya da amana da haɗin kai.

A wani labarin kuma, ministan ya duba wuraren horaswa da samar da kayan aikin kashin farko na jami’ai 800 a matsayin Runduna ta Musamman na Rundunar Sojin Nijeriya.

A wani ɓangare na shirye-shiryen horon, ministan ya duba wasu kayayyakin aiki a Sansanin Kabala waɗanda suka haɗa da masauki na ɗalibai da masu koyarwa, wuraren cin abinci, azuzuwa, tare da janareta don masu horarsa 44 da ake sa ran zuwan su.

Ya kuma duba wuraren harbin da aka inganta da sauran su domin horo, tare da cibiyar bayar da umarni na rundunar NIGCOY 2 ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNISFA) da aka sadaukar don aikin a Abyei, a Sudan ta Kudu.

Ministan ya ce ya gamsu da matakin aikin da aka yi a cibiyar, ya kuma ƙara jaddada aniyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na inganta ƙarfin soji da kuma bunƙasa al’adar ƙwarewa a cikin rundunar.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?