Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a ta Ƙasa (JAMB) ta ce sakamakon Jarrabawar Shiga Jami’a (UTME) ta shekarar 2024 ba ya shafin yanar gizon ta a halin yanzu.
Don haka hukumar ta yi gargaɗin cewa duk wani sakamako da aka buga a kan takardar ƙarya ce.
Mai magana da yawun JAMB, Dakta Fabian Benjamin, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, ya ce bayanin ya zama dole ne saboda tuni wasu mutane ke yaɗa sakamakon da aka buga a shafukan sada zumunta.
Benjamin ya ce sakamakon a halin yanzu ba ya nan kuma ba a iya samunsa a shafin yanar gizon JAMB, ba kamar shekarar da ta gabata ba.
Ya ce: “Hukumar na son bayyanawa ƙarara cewa hanya ɗaya tilo ta duba sakamakon UTME na 2024 ita ce aika UTMERESULT zuwa 55019 ko 66019, ta hanyar amfani da wayar da ɗan takarar ya yi amfani da ita wajen yin rijistar UTME.
“Wannan ya bambanta da abin da aka samu a shekarar da ta gabata, don haka, sakamakon, a halin yanzu, ba za a iya samunsa a shafin yanar gizon hukumar ba.
“Ana kira ga ‘yan takara da su bi hanyar da aka ƙayyade a sama domin samun sakamakonsu. Ba sa buƙatar ziyartar kafe ko biyan wani mutum kuɗi don bincika sakamakon su.
Ku tuna cewa Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a (JAMB) a ranar Litinin ta fitar da sakamakon Jarrabawar Shiga Jami’a (UTME) na shekarar 2024.