Back

Jami’an EFCC sun kewaye gidan Yahaya Bello da ke Abuja

Jami’an Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), a ranar Laraba, sun kewaye gidan tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, dake Wuse Zone 4 a Abuja.

Wani jami’in hukumar EFCC ya shaida cewa ana gudanar da aikin ne domin kamo tsohon gwamnan.

A baya dai hukumar EFCC ta gurfanar da Yahaya Bello, da ɗan uwansa Ali, da wani Dauda Suleiman, da kuma Abdulsalam Hudu a gaban Mai Shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya a watan Maris ɗin 2024 bisa zargin almundahanar naira biliyan 84.

Koƙarin jin ta bakin kakakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, ya ci tura.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?