Back

Jami’an Shari’a: Tinubu ya tunkari Majalisar Wakilai domin amincewa da sabon albashi da alawus

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rubutawa Majalisar Wakilai takardar neman amincewar albashi da alawus na jami’an shari’a.

Kakakin Majalisar, Abbas Tajudeen, wanda aka miƙa wa wasiƙar mai kwanan wata ranar 19 ga Maris, 2024 a ranar Talata ya karanta saƙon Shugaban Ƙasar yayin zaman majalisar, yana mai bayanin cewa ƙudurin dokar na neman sanya albashi da alawus da sauran fa’idodi ga jami’an shari’a.

Ya ce bitar kuɗaɗen da aka gabatar na da nufin kawo ƙarshen rashin ci gaba a albashinsu da kuma nuna haƙiƙanin yanayin zamantakewa da tattalin arziƙi na zamani.

Mai taken: ‘Ƙudirin dokar da ta tanadi albashi da alawus da sauran fa’idodi na ma’aikatan shari’a a Nijeriya da kuma abubuwan da suka shafe suʼ, Shugaban a cikin wasiƙar ya buƙaci a hanzarta yin nazari tare da zartar da shi.

“A bisa tanadin sashe na 58 (2) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya na 1999, (kamar yadda aka yi wa kwaskwarima), ina gabatar da, a nan, Ƙudurin Dokar Ma’aikatan Shari’a (Albashi da Alawus, da sauransu), 2024, don la’akarin Majalisar Wakilai.

“Ƙudurin Dokar Ma’aikatan Shari’a (Albashi da Alawus, da sauransu), 2024, na neman tsara albashi, alawus, da sauran fa’idodi ga jami’an shari’a, don kawo ƙarshen rashin ci gaba a albashinsu da kuma nuna haƙiƙanin yanayin zamantakewa da tattalin arziƙi na zamani.

“Ƙudirin dokar, wanda ya kafa sabon tsarin doka don biyan albashin jami’an shari’a, zai kuma tabbatar da ingantaccen ci gaba a cikin walwala, iyawa da ‘yancin kai na ɓangaren shari’a.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?