Back

Jami’an Tsaron Farin Kaya sun kama wata abokiyar hulɗar El-Rufai kan wani rubutu da tayi a Facebook kan Gwamna Sani

A ranar Lahadi ne jami’an tsaro da ake kyautata zaton Jami’an Tsaron Farin Kaya ne na hukumar DSS suka kama wata ‘yar siyasa kuma ‘yar jam’iyyar APC a Jihar Kaduna, Aisha Galadima.

An ce kamen na da nasaba da wani saƙo da aka wallafa a kafar sada zumunta na yanar gizo game da Gwamnan Jihar, Uba Sani.

A cewar majiyoyi, Galadima ta soki kalaman Gwamna Sani na ƙarshe akan tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Facebook.

Wata maƙwabciyarta ta ce an kama ta ne a unguwarsu da ke Tudun Wada a Kaduna a ranar Lahadi da yamma, kuma wata abokiyarta ta bayyana cewa an kashe wayar Galadima bayan an kama ta.

Sai dai Babban Sakataren Yaɗa Labarai na gwamnan, Muhammad Lawal Shehu, ya ce bai da masaniya game da kama ta, kuma ya ce a tuntuɓi Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) don ƙarin haske kan lamarin.

“Ban san cewa an kama wata mata da ta buga munanan kalamai akan Mai Girma Gwamna ba. Ko yaya dai ku miƙa tambayoyinku ga hukumar DSS ba Gwamnatin Jihar Kaduna ba,” inji shi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?