
Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, Wudil wadda aka sauyawa suna Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote, ta samar da wata na’ura mai amfani da mutum-mutumi da za ta baiwa ma’aikata damar gudanar da ayyukan cikin gida kamar tsaftacewa, share-share da sarrafawa a cibiyar.
Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Musa Yakasai, ya shaidawa manema labarai cewa na’urar mutum-mutumin za ta taimaka wa ma’aikatan wajen gudanar da ayyukan su yadda ya kamata.
Ya ce hukumar gudanarwar cibiyar ta samu ci gaba sosai kan fasahar kere-kere da amfani da fasahar sadarwa don baiwa dalibai damar yin amfani da fasahar gaba daya da kuma zama wani bangare na sauyin ayyukan na’ura na duniya.
Ya ce an riga an gwada na’urar mtum-mutumin kuma yana aiki da kyau kamar yadda aka tsara.
Ya ce jami’ar za ta samar da na’urori iri-iri da za su taimaka wajen rage ayyukan cibiyar.
Mataimakin shugaban jami’ar ya ce sabon dakin karatu da aka gyara yana da karfin daukar dalibai sama da 500 kuma yana da cikakkiyar alaka da yanar gizo da sauran kayan aikin na’urori.
Farfesa Yakasai ya ce duk da cewa jami’ar ta kirkiro wani dakin karatu na yanar gizo mai cikakken aiki, amma ana karfafa wa dalibai gwiwa da su ci gaba da tsarin dakin karatu na yau da kullun don inganta al’adun karatuttukan su.