Hukumomin Jami’ar Ilorin (UNILORIN), a jihar Kwara, a ranar Litinin, sun ce sun kori tare da dakatar da wasu ɗalibai 19, ciki har da ɗaliban matakin ƙarshe guda shida a jami’ar bisa samunsu da hannu a laifuka mabanbanta.
A wata sanarwa da Daraktan Kula da Harkokin Jami’ar, Kunle Akogun, ya fitar, ya bayyana cewa Mataimakin Shugaban Makarantar, Farfesa Wahab Egbewole (SAN), ya amince da korar ɗaliban da abin ya shafa biyo bayan shawarar Kwamitin Ladabtarwa na Ɗalibai a taron sa na 220/221.
Sanarwar ta ce an hukunta ɗaliban da lamarin ya shafa kan laifuffuka da suka haɗa da rashin ɗa’a, sata, maguɗin jarrabawa, sayar da wurin gadon ɗakin kwanan ɗalibai ba bisa ƙa’ida ba, dukan wani ɗalibin su, karɓar kuɗi ta hanyar barazana, da kuma cin zarafi.
Har ila yau, ya ce hukunce-hukuncen laifukan da ɗaliban suka aikata sun haɗa da dakatarwa ko dai na zango ɗaya ko kuma na shekaran karatu ɗaya, ciki har da kora.
Ɗaliban da abin ya shafa sun kasance a matakai daban-daban na ilimi da suka haɗa da matakan 100, 200, 300 da 400.