Back

Jami’in Hukumar Kwastam ya kashe kansa a Abuja

Wani jami’in Hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS) dake aiki a Babban Birnin Tarayya, Abdulwahab Magaji, ya harbe kansa har lahira a gidansa da ke Abuja.

An ruwaito cewa Magaji ya kashe kansa da bindiga a gidansa da ke kan titin Binta a unguwar Farm Estate, Abuja.

An kuma ce dangin Magaji sun kai rahoton mutuwarsa ga ‘yan sanda, lamarin da ya sa jami’an suka mamaye wurin da lamarin ya faru.

Wata majiyar iyalinsa ta ce a lokacin da ‘yan sanda suka isa wurin, an garzaya da mamacin zuwa asibiti, inda aka tabbatar da mutuwarsa.

Majiyar ta ci gaba da cewa, “Wani daga iyalin mamacin ne ya sanar cewa CSC Abdulahi Abdulwahab Magaji, jami’in kwastam dake aiki a Abuja, ya harbe kansa a gidansa da ke Farm Centre da bindiga.

“Jami’an ‘yan sanda sun garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka kai wanda aka kashen zuwa asibiti, inda likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da mutuwarsa.”

Majiyar ta ƙara da cewa an miƙa gawar mamacin ga iyalinsa domin binne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?