Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Nijeriya (SSANU) ta shiga yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai, daga ranar Litinin.
Hakan ya biyo bayan ƙin biyan buƙatun ƙungiyar da Gwamnatin Tarayya ta yi.
An ruwaito cewa, wani ɓangare na batun yajin aikin shine sake tattaunawa kan yarjejeniyar 2009 – batun ƙarin albashi da kashi 25/35 cikin 100 na mafi ƙarancin albashi da kuma batun naira biliyan 50 da gwamnati ta yi alƙawarin bayarwa a matsayin alawus.
Shugaban Ƙungiyar na reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK), Mustapha Aminu, ya ce a wani taron gaggawa na Majalisar, an amince da a ci gaba da yajin aikin.
“Taron na daga cikin umarnin hukumar ta ƙasa cewa ya kamata mu kira taron gaggawa saboda za mu fara yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai daga ranar 18 ga wannan watan, kuma yanzu za ka ga kusan kowa na goyon bayan wannan yajin aiki, don haka tabbas ba za mu huta ba.
“Ya zuwa ranar 18 ga watan Maris idan gwamnati ba ta ce komai ba to mun riga mun shiga yajin aikin.
“A halin yanzu gwamnati ba ta yi komai ba don haka muna jiran gwamnati ta mayar da martani idan ba haka ba yaren da kawai suke fahimta shi ne yajin aiki kuma a shirye muke mu shiga.
“Bayan yajin aikin gargaɗi na kwana bakwai, za mu shiga yajin aikin sai baba ta gani.”