Jam’iyyar Labour ta yi kira da a kamo Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC), Joe Ajaero, bisa wani hari da aka kai wa sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa a Abuja ranar Laraba.
A safiyar ranar ce wasu ‘yan ƙungiyar NLC suka kai farmakin domin nuna adawa da babban taron jam’iyyar na ƙasa da aka shirya gudanarwa a ƙarshen watan Maris.
Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar Labour na Ƙasa, Kwamared Arabambi Abayomi, a yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abeokuta, a ranar Laraba, ya bayyana harin a matsayin wani shirin tayar da ƙayar baya na siyasa ga Gwamnatin Tarayya ta hanyar wani hali da ka iya haifar da rashin zaman lafiya a ƙasar.
Ya kuma bayyana farmakin a matsayin wani yunƙuri daga Ƙungiyar Ƙwadago da Kwamared Ajaero ke jagoranta na karɓe jam’iyyar Labour da ƙarfin tsiya ta hanyar ‘juyin mulki’ domin hamɓarar da shugabancin jam’iyyar.
Ya zargi shugaban NLC da yunƙurin naɗa wani Ladi Iliya daga Arewa a matsayin muƙaddashin shugaban LP, da Kenneth Okwonko a matsayin muƙaddashin sakataren na ƙasa domin cimma burinsa na shugaban ƙasa a 2027.
Sai dai Arabambi ya yi kira ga Sufeto Janar na ‘Yan Sanda da Darakta Janar na DSS da su kama Joe Ajaero bisa zargin cin amanar ƙasa.
“Mun damu da matakin da Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya, NLC, ƙarƙashin jagorancin Kwamared Ajaero ta ɗauka na ƙwace jam’iyyar da ƙarfi da yaji wanda suka yi a yau kamar juyin mulki da nufin hamɓarar da shugabancin jam’iyyar mu domin cimma burinsa na Shugaban Ƙasa a 2027 wanda ba zai taɓa yiwuwa ba a jam’iyyar Labour,” inji shi.