Back

Jam’iyyar Labour ta goyi bayan Ningi kan ƙarin kasafin kuɗi

Sanata Abdul Ningi

Jam’iyyar Labour (LP) ta yaba wa Sanata Abdul Ningi, da ya yi magana kan zargin ƙarin naira tiriliyan 3 a cikin kasafin kuɗin 2024, inda ta ce Sanatocin LP a Majalisar Wakilai ta 10 sun yarda da shi.

Prince Kennedy Ahanotu, Shugaban Matasan jam’iyyar LP na Ƙasa ne ya bayyana haka a jiya yayin wata ziyarar haɗin kai da matasa suka kai a sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa a Abuja.

Majalisar ta dakatar da Sanata Ningi mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa na tsawon watanni uku a ranar Talata kan zargin da ya yi na ƙarin sama da naira tiriliyan uku a kasafin 2024.

Ahanotu ya ce, “Sanatoci da dama baya ga Sanatocin jam’iyyar Labour sun marawa ɗan majalisar da aka dakatar saboda jajircewarsa.

“Akwai mutane da yawa da suka goyi bayansa, amma shi ne aka ba damar maganar.

“Amma ina tabbatar muku cewa da yawa daga cikin Sanatoci ciki har da Sanatocin jam’iyyar Labour suna mara masa baya saboda yana ƙoƙarin bankaɗo matsalolin da Majalisar Dokoki ta ƙasa ke fuskanta.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?