Back

Jam’iyyar NNPP ta Lashe Zabukan Majalisar Jiha Guda Biyu A Kano

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta bayyana Alhassan Ishaq na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi ranar Asabar a mazabar Kura/Garun Mallam a jihar Kano.

Jami’in zaben Farfesa Shehu Galadanchi ya bayyana cewa Ishaq na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 37,262 inda ya doke Musa Daurawar na jam’iyyar All Progressives Congress, wanda ya samu kuri’u 30,803.

A baya, Kotun daukaka kara ta umurci INEC da ta sake gudanar da zabe a rumfunan zabe 20 da ke mazabar Kura/Garun Malam a jihar Kano.
Hakazalika, INEC ta ayyana Bello Butu-Butu na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi ranar Asabar a mazabar Rimin Gado/Tofa.

Jami’in zabe, Farfesa Ibrahim Tajo Suraj ya kuma bayyana cewa Bello Butu-Butu na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 31,135 inda ya doke abokin hamayyarsa na APC wanda ya samu kuri’u 25,577.

Kotun daukaka kara ta kuma umurci INEC da ta sake gudanar da zabe a rumfunan zabe 33 da ke mazabar Rimin Gado/Tofa.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?