Back

Jihar Zamfara Za Ta Kashe Naira Biliyan Uku Akan Ayyukan Shawarwari daTuntuba 

Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal za ta kashe Naira biliyan uku a matsayin “kudin biyan tuntuba na ayyukan gwamnati da shirye-shirye” a shekarar nan in ji SaharaReporters.

Adadin yana kunshe ne, kamar jaridar ta wallafa, a cikin kasafin kudin jihar na shekarar na Naira biliyan dari hudu da ashirn da shida wanda gwamna Dauda Lawan ya gabatarwa wa Majalisar dokokin Jihar, Kuma gwamnan ya sanya wa hannu a watan sha biyu na shekarar da ta gabata.

Adadin, kamar yadda jaridar ta wallafa, yana kunshe ne a cikin kasafin kudin jihar na shekarar nan wanda aka yi wa lakabi da “kasafin Ceto.”

Saharareporters ta ce, an ware Naira biliyan dari da sha takwas domin gudanar da ayyukan gwamnati akai-akai, wanda aka misalta ya kai kashi ashirin da bakwai cikin dari na adadin kasafin kudin, sannan kuma an ware Naira biliyan dari uku da takwas wanda ya kai kashi saba’in cikin dari na kasafin kudin da burin za a kashe su a manyan Ayyukan gwamnati.

Binciken Saharareporters, ya nuna cewar kasafin kudin ya nuna cewa an ware naira miliyan dari tara da hamsin domin gina fadar sarakunan gargajiya guda tara. 

Sarakunan Anka, Bungudu, Maru, Tsafe, Kaura, Namoda, Moriki, Bukkuyum da Bakura.

Gwamnatin ta ayyana zata gina masallatai a dukkan kananan hukumomi goma Sha hudu na jihar kuma za ta kashe Naira miliyan dari biyu yayin da kuma za a yi amfani da wasu Naira miliyan dari da hamsin a wajen gina makabartu.

Saharareporters ya ruwaito cewa, “Zamfara kamar wasu sauran jihohin Arewa maso Yamma, ta fuskanci munanan hare-hare daga ‘yan bindiga a cikin shekaru goma da suka gabata.”

A shekara ta dubu biyu da sha tara, gwamnatin jihar ta taba kulla yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan bindigar da ke addabar Jama’a.

“Kimanin sabbin motoci kirar Hilux guda goma Sha biyar ne da kuma kyaututtuka na kudade ga shugabannin kungiyoyin ‘yan ta’adda da suka tuba, gwamnatin ta bayar daga hannun tsohon gwamnan jihar kuma karamin ministan tsaro na yanzu, Bello Matawalle a shekarar dubu biyu da ashirin.”

“Amma duk da wadannan, an kai hari ga al’ummomin jihar tare da yin garkuwa ko kashe mazauna yankin.”

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?