Back

Jin Daɗin Ku Shine Mafi Muhimmanci, Karamar Ministan Abuja ta Gayawa ‘Yan Bautar Ƙasa

Karamar Ministar Babban Birnin Tarayya Babban (FCT), Mariya Mahmoud, ta tabbatar wa ‘yan bautar ƙasa da aka tura zuwa babban birnin tarayyan cewa jin daɗin su shine mafi muhimmanci ga gwamnati ta hanyar amfani da kayan aikin da ke hannun su.

Ta bayyana hakan ne a yayin bikin buɗewa da rantsar da ‘yan bautar ƙasar Kashi na ɗaya na shekarar 2024 da aka tura zuwa babban birnin tarayya Abuja domin gudanar da kwas ɗin wayar da kai a sansanin Hukumar Yiwa Ƙasa Hidima (NYSC) na dindindin da ke Kubwa, Abuja ranar Talata.

Ƙaramar Ministar wadda ta samu wakilcin Sakataren Umarni, na Sakatariyar Cigaban Jama’a, Ibrahim Aminu, ta ce, “Gwamnatin Babban Birnin Tarayya ta ƙuduri aniyar baiwa hukumar NYSC cikakken goyon bayan da ya kamace ta, ganin irin rawar da hukumar ke takawa a matsayin babbar abokiyar haɗin gwiwa wajen ci gaba na Babban Birnin Tarayya.”

Ta umurci masu bautar ƙasan da su yi amfani da shirin don ba da gudummawa ga ci gaban al’ummomin da zasu ƙarbi baƙuncin su.

“A nan FCT, matasanmu da matanmu da yawa suna buƙatar tallafin ku, na yi imanin za ku taimaka musu su bunƙasa basirarsu daban-daban don yin ƙirkire-ƙirkire,” in ji ta.

A nata ɓangaren, mai gudanarwar NYSC FCT, Mrs, Winifred Shokpeka, ta sanar da cewa, an yi wa mutane dubu uku da ɗari takwas da casa’in da ɗaya rijista don kwas ɗin wayar da kan, wanda ya ƙunshi maza dubu ɗaya da ɗari huɗu da tamanin da ɗaya da mata dubu biyu da ɗari biyar da goma. Ta kuma gargaɗi ‘yan bautar ƙasar da su nisanci munanan ɗabi’u kamar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da sauran abubuwan da suka saɓa wa zamantakewa a ciki da wajen sansanin.

Shokpeka ta umarce su da su ba da himma da ayyukan sansanin tare da miƙa wuya ga horon da ke tattare cikin dokokin shirin.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?