Wani jirgin sama mallakin wani kamfanin jiragen sama na Xejet, ya zarce titin jirgi ya faɗa cikin ciyayi a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas.
Jirgin mai lamba Embraer 145 ɗauke da fasinjoji 52 da ma’aikatansa ya tashi daga filin jirgin Abuja kafin faruwar lamarin.
A cewar majiyoyi a filin jirgin, an rufe titin saukar jiragen sama na 18L da jiragen ke zirga-zirga a yayin da jami’an Sashen Ceto da Kashe Gobara ta Aerodrome na Hukumar Kula da Filayen Tashi da Saukar Jiragen Sama ta Nijeriya (FAAN) suka yi tattaki zuwa wurin da lamarin ya faru domin ceto fasinjojin.
“Wani jirgin na kamfanin jiragen sama na Xejet ya zarce daga titin jirgi a filin jirgin saman Legas. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:29 na safe, yayin da jirgin ya kutsa cikin gabar ciyawa ta B5.
“Ma’aikatan kashe gobara da ceto suna nan don taimakawa wajen kwashe fasinjojin.
“A halin yanzu an rufe Runway18L daga zirga-zirga,” inji majiyar.