Wani jirgin ƙasa da ya taso daga Kaduna zuwa Abuja ya kauce a tsakiyar hanyar zuwa babban birnin ƙasar ranar Lahadi.
Blueprint ta gano cewa jirgin mai ɗauke da fasinjoji da dama ya bar Kaduna ne da misalin ƙarfe 8 na safe amma bayan kusan awa ɗaya, kociyoyi kusan 3 suka kauce hanya.
An baza jami’an tsaro da sojoji wurin da lamarin ya faru, an kuma ga injiniyoyin jirgin na ƙoƙarin gyara sassan titin jirgin ƙasan da suka lalace.
Ko da yake ana dakon sanarwar a hukumance, amma majiyoyi sun shaida cewa ba a samu asarar rai ba a yayin da lamarin ya faru.