Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta ce a ranar 15 ga Mayu, 2024 za a fara ɗaukar maniyyatan Nijeriya zuwa ƙasar Saudiyya don aikin hajjin bana.
Shugaban Hukumar NAHCON, Malam Jalal Ahmad Arabi ne ya bayyana haka a jawabinsa na buɗe Babban Taron Masu Ruwa Da Tsaki Na Harkar Hajji da Umrah na Nijeriya na farko da aka gudanar a Cibiyar Shehu Musa Yar’adua da ke Abuja.
Arabi ya ce kusan maniyyatan Nijeriya 65,500 ne za su yi aikin Hajjin shekarar 2024, inda ya ce kamfanonin jiragen sama da aka amince da su ne za su ɗauke su daga cibiyoyi 10 na tashin jiragen sama na ƙasar.
Shugaban Hukumar NAHCON ya ce hukumar ta yanke shawarar cewa a aikin na bana, dukkan alhazan Nijeriya za su ziyarci kuma su shafe aƙalla kwanaki huɗu a Madina kafin a fara aikin Hajjin yadda ya kamata.
Da yake magana kan taron, Arabi ya ce haɗuwar masu ruwa da tsaki wani nauyi ne da Allah ya ɗora wa kowa, yana mai cewa taken taron, “Haɗin kai, Hadin Gwiwa da Aikin Gayya: Abubuwa uku don nasara na ayyukan Hajji na 2024” an zaɓe shi cikin tsanaki.
Ya ce hukumar alhazan ta ga ya dace ta tattauna da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da gudanar da aikin Hajjin cikin nasara.
Ya ƙara da cewa yana da kyau duk masu ruwa da tsaki su haɗa kai domin alhazai su yi aikin hajji mai kyau a bana.