Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta yi nasarar jigilar maniyyata sama da 1,600 zuwa ƙasar Saudiyya domin aikin hajjin bana.
Kashi na baya-bayan nan, wanda ya ƙunshi maniyyata 515, sun tashi ne a ranar Lahadi ta kamfanin jirgin Max Air, mai jigilar maniyyatan Kaduna.
Yunusa Muhammad, Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa.
Ya ce hakan ya kawo adadin maniyyatan da aka ɗauko daga jihar zuwa 1,612.
Ya ce a halin yanzu an fara tantance maniyyatan da aka shirya wa jirgi na huɗu a sansanin jigilar alhazan da ke Mando, Kaduna, kuma a yau ne ake shirin tashi.