
Gwamna Abba da Ganduje
Shugaban jam’iyyar APC mai mulki na ƙasa, Dakta Abdullahi Ganduje, ya ja kunnen Gwamna Abba Yusuf na Jihar Kano da ya daina amfani da dabarun karkatar da hankulan jama’a don ɓoye gazawar sa wajen yi wa al’ummar jihar aiki.
Ganduje, a cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun Babban Sakataren Yaɗa Labaransa, Edwin Olofu, ya bayyana sabbin zarge-zargen da gwamnan ke yi a matsayin wani yunƙuri mai ban takaici na karkatar da hankula daga ayyukan sa.
Tsohon gwamnan na Jihar Kano ya zargi magajinsa da cewa ba shi da komai a ƙasa domin tabbatar da ƙarin kuɗaɗen kason da dokar ƙasa ta yi wa jihar tun ranar 29 ga watan Mayun 2023 lokacin da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya hau mulki.
Shugaban jam’iyyar APC na mayar da martani ne kan matakin da Gwamnatin Jihar Kano ta ɗauka na gurfanar da shi a gaban kotu bisa zarginsa da cin hancin dalar Amurka 413,000 da kuma naira biliyan 1.38 a lokacin da yake gwamna.
Ya bayyana cewa sabon yunƙurin da jihar ta yi na ɓata sunansa ba zai yi nasara ba, ya ƙara da cewa hakan ya nuna jahilci da rashin bin doka da oda daga gwamnatin da Gwamna Yusuf ke jagoranta na fara tuhumar sa.
“A cikin yunƙurin da suke yi ido rufe na cin zarafi na da iyalina, ko dai sun manta ko kuma ba za su iya gudanar da kansu bisa ga umarnin doka ba.
“Sun kasa ɗaukar matakin shari’a kan sanarwar da Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta yi kwanan nan, inda ta ce laifin da ake zargina da shi, laifin tarayya ne wanda Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya da kuma Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ne kawai zasu iya gurfanarwa.
“Maimakon in tsaya rigima da masu cin zarafi na a Kano kan zargin ƙarya da ake yi mani, zan roƙe su da su karkato da ƙarfin su wajen rage raɗaɗin al’ummarmu a Kano.
“Har yanzu suna da damar komawa kan tsarina na ci gaba mai ɗorewa da ci gaban jihar Kano. Har yanzu bai makara ba su yi koyi da ci gaban da na samu. Har yanzu za su iya ceto lamarin domin a zamanina ba a yi wani laifi ba,” inji Ganduje.
Shugaban jam’iyyar APC wanda ya mulki jihar Kano a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023, ya kuma yi maraba da matakin da gwamnatin ta ɗauka na kafa kwamitoci guda biyu domin gudanar da bincike a kansa kan zargin almubazzaranci da dukiyar jama’a, tashe-tashen hankulan siyasa da kuma mutanen da suka ɓace.
Sai dai ya lura cewa zai fi dacewa a ƙara wa’adin binciken daga shekarar 1999 zuwa yau.
“Kamar yadda ake cewa, wanda ya zo ga adalci dole ne ya zo da hannuwa masu tsafta. Bai kamata a ga an tuhume gwamnatina kaɗai ba. Bai kamata a ga an yi hakan don ƙeta, ramuwar gayya da mugun nufi ba. Kamata ya yi don amfani da maslahar jama’a ne.
“Mun gudanar da al’amuran mulki a jihar a bayyane a lokacin da nake mulki. Ba mu buƙatar jagoranci daga iyayengiji don yin abin da ya dace,” inji Ganduje.