Back

Ka dakatar da tallafin wutar lantarki yanzu, inji Hukumar Ba Da Lamuni ta Duniya ga Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu

Hukumar Ba Da Lamuni ta Duniya (IMF) ta gargaɗi Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ya cire abin da ta kira tallafin man fetur da wutar lantarki a fakaice.

A cikin wani rahoto da IMF ta wallafa kwanan nan, Hukumar ta shaida wa Tinubu cewa tallafin zai cinye kashi uku cikin 100 na ɗaukacin darajar kayayyakin da aka samar a ƙasar nan a shekarar 2024 saɓanin kashi ɗaya cikin ɗari a shekarar da ta gabata.

A cewar rahoton, IMF ta yaba wa Gwamnatin Tarayya da ta kawar da “tallafin makamashi mai tsada da kuma koma baya”, tana mai cewa wannan yana da matuƙar muhimmanci wajen samar da kuɗi don ci gaba da kuma ƙarfafa kariyar zamantakewa tare da kiyaye ɗorewar bashi.

IMF ta lura cewa, duk da haka, “ba a haɓaka isassun matakan ramawa ga talakawa ba kuma daga baya an dakatar da su saboda matsalolin cin hanci da rashawa. Iyakance farashin man fetur ƙasa da farashinsa ya sake dawo da tallafin a fakaice a ƙarshen shekarar 2023 domin taimakawa ‘yan Nijeriya shawo kan hauhawar farashin kayayyaki da faɗuwar farashin canji.”

Kamfanin Mai na Nijeriya da Ƙaramin Ministan Man Fetur Heineken Lokpobiri sun sha musanta iƙirarin cewa Gwamnatin Tarayya na biyan tallafin man fetur ta ƙofar baya.

Kiran da IMF ta yi na cire tallafin wutar lantarki na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan Nijeriya ke zanga-zangar neman Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, da ya mayar da kuɗin lantarki na Band A kamar yadda yake a baya.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?