Back

Kaduna: ‘Yan Shi’a sun zargi Gwamna Sani da ‘yan sanda kan kashe ‘yan uwansu, sun kai ƙara Majalisar Dattawa

‘Yan Shi’a sun sake kai ƙara wurin Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, bisa zargin kashe-kashen da Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, da kuma Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar, Mista Ali Audu Dabigi, suka yi ba bisa doka ba.

Sun kuma shigar da ƙara wurin Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, da Shugaban Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda (PSC), Mista Solomon Arase, kan hare-haren da suke zargin sun kai ga kashe ‘yan uwansu.

Koken da taron ya gabatar wa manema labarai a Abuja mai kwanan ranar 23 ga Afrilu, 2024 ne kuma Shugaban Dandalin, Farfesa Abdullahi Danladi ne ya sanya wa hannu.

Wasiƙun, mai taken: “Koke kan Mista Uba Sani, Gwamnan Jihar Kaduna da Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kaduna kan kisan gillar da aka yi wa mutane bakwai tare da raunata sama da 30 na masu zanga-zangar lumana a ranar 5 ga Afrilu, 2024 a Kaduna da Zariya, ” an gabatar da shi ga manema labarai ranar Lahadi a Abuja

Kwafin takardar koken da aka rubuta wa Shugaban Majalisar Dattawa ya ce: “Mun rubuta zuwa ofishin ku don sanar da ku game da yadda Gwamnan Jihar Kaduna da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kaduna suka baiwa Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya umarnin ta buɗe wuta kan masu zanga-zangar lumana na goyon bayan Falasɗinawa a Kaduna da Zariya a ranar 5 ga Afrilu, 2024.

“Rikicin Gabas ta Tsakiya tsakanin Falasɗinu da Isra’ila lamari ne na duniya wanda ya mamaye duniya da ayyukan Majalisar Ɗinkin Duniya tun daga Oktoba 2023.

“Wannan lamarin ya haifar da zanga-zangar adawa kan kisan gillar da sojojin Isra’ila suka yi wa fararen hula a zirin Gaza.

“Ana ta zanga-zanga ba tare da tsayawa ba a Amurka, Burtaniya, Faransa, Jamus da sauran ƙasashen Turai, gami da ita kanta Isra’ila.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?