Back

KAEDCO ta ware naira miliyan 350 don bunƙasa wutar lantarki a Kaduna

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kaduna, KAEDCO, ta ware naira miliyan 350 don inganta tashar wutar lantarki da ke Millennium City a wani yunƙuri na kawo ƙarshen katsewar wutar lantarki da ake fama da shi a wasu sassan birnin Kaduna.

Babban Jami’in Gudanarwa (COO), na KAEDCO, Abubakar Sadiq Mohammed, ne ya bayyana hakan a Kaduna ranar Juma’a bayan ya kai na’urar taransifoma 7.5MVA da aka sayo kwanan nan domin sawa a Millennium City, Kaduna.

Babban Jami’in Gudanarwan ya bayyana cewa, kamfanin ya fara zuba jarin ne domin magance matsalolin samar da wutar lantarki da ya shafi abokan ciniki sama da 20,000 a wasu unguwanni bakwai da ke cikin Millennium City da kewaye.

“Taransifomar wutar lantarki mai ƙarfin 7.5MVA ɗaya tilo da ke cikin tashar da layin 11KV da ake da su duka an yi musu nauyi sosai kuma ba za su iya biyan buƙatun wutar lantarki na kwastamomi ba.

Don haka, wannan aiki na miliyoyin naira, an yi shi ne don magance waɗannan ƙalubale da kuma kawo gagarumin sauƙi ga abokan cinikinmu da ke yankunan Kadaure, Keke (A da B), Dan Hono, Kadage, Dan Bushiya da Sabon Gida, duk a cikin Millennium City. Kaduna,” inji shi.

“Bayan kammalawa, za a haɓaka ƙarfin tashar zuwa 2 × 7.5MVA tare da ƙarin sabon layin 11KV. Za a fara aikin sanyawa da gina sabon na’urar samar da lantarki mai ƙarfin 11KV a mako mai zuwa kuma muna fatan ƙaddamar da aikin cikin ƙanƙanin lokaci, “inji Mohammed.

Ya yi kira ga kwastomomi a cikin al’ummomin da abin ya shafa da su mayar da martani ga ƙoƙarin Kamfanin ta hanyar sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.

“Ina so in yi amfani da wannan hanyar don yin kira ga abokan cinikinmu da su sauke nauyin da ke kan su na biyan kuɗin wutar lantarki. Wannan ita ce hanya ɗaya tilo a matsayinmu na kamfani da za mu iya sauke nauyin da ya rataya a wuyanmu na kasuwanci,” inji shi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?