Back

Kakakin Majalisa, mataimakinsa, Buhari na taya Tinubu murnar cika shekaru 72

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajuddeen da mataimakinsa, Benjamin Kalu sun taya Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekaru 72 da haihuwa.

Sun taya Shugaban Ƙasar murnar ne a cikin saƙonni daban-daban na taya murna ranar Alhamis.

A cikin saƙon taya murna da sa hannun Mai Ba Shi Shawara na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Musa Abdullahi Krishi, Kakakin Majalisar ya bayyana shugaban a matsayin “jigon siyasar ci gaba”, inda ya ƙara da cewa shugaban ya inganta siyasa da mulki a Nijeriya.

Hakazalika, Mataimakin Shugaban Majalisar, Benjamin Kalu a cikin saƙonsa mai ɗauke da sa hannun Babban Sakataren Yaɗa Labaransa, Levinus Nwabughiogu, ya yabawa shugaba Tinubu bisa irin matakan da ya ɗauka na zahiri wanda a yanzu ke taimakawa tattalin arziƙin ƙasar ya farfaɗo.

Hakazalika, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya kuma bayyana Shugaba Tinubu a matsayin jagora mai hangen nesa, inda ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su mara masa baya a yunƙurinsa na magance yawaitar ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.

Sanata Barau a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis ta hannun Mai Ba Shi Shawara na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Ismail Mudashir, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi wa ƙasa addu’a.

Har ila yau, tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya miƙa gaisuwa ga Shugaba Tinubu, a bikin cikarsa shekaru 72 a duniya, inda ya yabawa Shugaban Ƙasar bisa ƙoƙarin da yake yi na shawo kan ƙalubalen da ƙasar nan ke fuskanta.

Buhari a cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawunsa, Malam Garba Shehu ya fitar, ya yi addu’ar Allah ya ba Shugaban Ƙasar lafiya da tsawon rai domin ƙasar ta ci gaba da cin gajiyar “kyakkyawan shugabancinsa.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?