Back

Kakakin Shugaban Ƙasa ya ce ba a buƙatar zanga-zanga akan yunwa

Mai baiwa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Ajuri Ngelale, ya caccaki Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) kan gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar inda ya ce hakan ba abun buƙata ba ne.

Biranen Najeriya sun gudanar da zanga-zangar lumana a ranar Talata yayin da ‘yan ƙungiyoyin ƙwadago suka mamaye titunan ƙasar domin nuna rashin amincewa da wahalhalun tattalin arziƙi da hauhawar farashin kayayyaki da ke addabar al’ummar ƙasar.

Ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ta yi na dakatar da zanga-zangar a cikin mintunan ƙarshe ya ci tura.

Shugaban NLC, Joe Ajaero ne ya jagoranci zanga-zangar da aka gudanar a Abuja, Legas, Ibadan, Jos da sauran manyan biranen ƙasar.

Daga cikin fitattun ‘yan Najeriya da suka halarci zanga-zangar sun haɗa da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde; lauyan kare haƙƙin ɗan Adam, Femi Falana; ɗan takarar shugaban ƙasa na African Action Congress, Omoyele Sowore, da sauran su.

Da yake mayar da martani kan zanga-zangar, mai magana da yawun shugaban ƙasar ya ce tuni gwamnatin tarayya ta fara magance wahalhalun da ake fuskanta.

Ngelale ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da gidan talabijin na TVC inda ya ƙara da cewa rashin shiga zanga-zangar da Ƙungiyar Ƙwadago ta ‘Yan Kasuwa (TUC) ta yi ya nuna babu buƙatar hakan.

“Duk wata ƙungiyar ƙwadago da ke magana akan damuwar iyalan Najeriya, raɗaɗin da mutanenmu ke ji, tana da ’yancin yin hakan. Ya dace ‘yan Najeriya su yi magana a cikin mawuyacin hali,” inji shi.

“Kuma gwamnati ta yi duk mai yiwuwa don ganin an shawo kan matsalolin. Sai dai kuma muna son raba damuwar da wasu ƙungiyoyin ƙwadago ke bayyanawa da mutanen da ke ƙoƙarin yin amfani da wasu al’amura a ƙasar don cimma wata manufa ta siyasa.

“Mun ga Ƙungiyar Ƙwadago ta ‘Yan Kasuwa (TUC) ta janye daga zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar. Mun ga Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙasa (NANS) ta fice daga zanga-zangar. Babu haɗin kai kan abin da NLC ke ƙoƙarin yi. Na yi imanin duk wasu damuwa da ƙungiyoyin ƙwadago ke tadawa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na ƙoƙarin shawo kansu.”

Zanga-zangar wacce gargaɗi ce na kwanaki biyu ga gwamnatin tarayya za ta cigaba gobe.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?