Manajan Daraktan Kamfanin Jiragen Ƙasa na Najeriya (NRC), Injiniya Fidet Okhiria, ya bayyana shirye-shiryen faɗaɗa ayyukan kamfanin da samar da ababen more rayuwa domin inganta hanyoyin sufuri da haɗin hanyoyi a faɗin Najeriya.
Ya shaida wa manema labarai a wajen wani taron kwana biyu na ministoci tare da Ministan Sufuri a Abuja, cewa za a fara gudanar da ayyuka a kan hanyar Legas zuwa Kano, tare da mai da hankali kan ƙarfafa tawagar jiragen ƙasan.
Okhiria ya ce ya kamata matafiya su sa ran fara ayyuka a hanyar Fatakwal zuwa Aba a cikin wata biyu masu zuwa, tare da yin alƙawarin ƙara samun sauƙi.
Okhiria ya jaddada gagarumin ci gaban da aka samu a kan hanyar Kaduna zuwa Kano, inda aka maida hankali wajen daidaita matsattsen titin jirgi da daidaitaccen titi.
Kammala wannan jeri, a halin yanzu ya kai kaso tamanin cikin dari, wanda ake sa ran zai sauƙaƙe ayyuka da inganta sauyin hanyoyi ga fasinjoji daga Makarfi zuwa Kano. Bugu da ƙari, ayyukan jerr-jeren hanyoyin daga Maƙarfi zuwa Kaduna na nuna tsayayyen ci gaba da aka samu wajen kammalawa,” in ji shi.
Okhiria ya bayyana fatan shi na cewa, sai dai idan an samu ƙalubalen da ba a yi tsammani ba, amma hanyar Abuja zuwa Kaduna za ta iya kammaluwa ta kuma fara aiki a tsakiyar shekara mai zuwa.
Injiniya Okhiria ya bayyana ƙwarin gwiwar shi na cewa kamfanin jiragen kasan na iya tsawaita hanyoyi da za su wuce Kaduna, tare da hasashen tafiya daga Abuja zuwa Kano a tsakiyar shekara mai zuwa.
Ya ce, “Wannan kyakkyawan hangen nesan na nuna aniyar hukumar na inganta ababen more rayuwa na sufuri da bunƙasar tattalin arziƙin ƙasa baki ɗaya.
Kamar yadda kamfanin ke ba da fifikon faɗaɗawa da ƙoƙarin tafiya da zamani, waɗanda ke nuna kyakkyawan ci gaba ne ga sufurin jiragen ƙasa a Najeriya, ya kuma magance buƙatun jama’a da haɓaka ci gaban zamantakewa da tattalin arziƙi a faɗin ƙasar.