Back

Kamfanin jiragen sama na Emirates zai dawo da tafiye-tafiye zuwa Nijeriya a watan Yuni, inji Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, a watan Yunin bana ne ake sa ran kamfanin jiragen sama na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Emirates, zai dawo da tafiye-tafiyen jiragensa zuwa Nijeriya.

Wannan dai na zuwa ne kusan shekaru biyu bayan da kamfanin ya dakatar da tafiye-tafiyen jiragen sama zuwa Nijeriya bisa wasu matsaloli tsakanin ƙasashen guda biyu da suka shafi wasu kuɗaɗe da suka maƙale da dai sauransu.

Emirates ya sanar da dakatar da tafiye-tafiyen jiragenta zuwa Nijeriya daga ranar 1 ga Satumba, 2022.

Sai dai kuma Ministan Sufurin Jiragen Sama, Mista Festus Keyamo yayin da ya bayyana a Shirin Safiya na gidan talabijin na Arise a ranar Litinin ya ce, “Dawowar tafiye-tafiyen jiragen Emirates ya kusa faruwa. Ban daɗe da samun saƙo daga Emirates ba. Saƙon na kan wayata yanzu. A shirye suke su dawo.

Ministan ya kuma yi nuni da cewa, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya taka rawar gani wajen warware matsalolin da ke tsakanin ƙasashen biyu.

“Ina sanar da ‘yan Nijeriya a karon farko; cewa ban daɗe da samun saƙo daga Emirates ba. Saƙon na tare da ni. Za su bayyana ranar da za su yi tafiyar su na gaba. Mun samu wani saƙo da ke tabbatar da cewa an warware dukkan matsalolin kuma an shirya fara dawowa. Yana iya kasancewa kafin watan Yuni.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?