Back

Kashi 95 cikin ɗari na masu aƙidar Boko Haram sun mutu, inji gwamnatin Borno

Gwamnatin Jihar Borno ta ce sama da kashi 95 cikin ɗari na mutanen da ke da aƙidar Boko Haram, musamman waɗanda suka kafa ta, ko dai sun mutu ko kuma sun miƙa wuya.

Mai bai wa gwamnatin jihar shawara ta musamman kan harkokin tsaro, Birgediya-Janar Ishaq Abdullahi (ritaya), shi ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a Maiduguri a ranar Lahadi.

Ya ce shugabannin ƙungiyar na cikin ruɗani domin kusan mutum 10 ne kawai daga cikin waɗanda suka kafa ƙungiyar ke raye.

Abdullahi ya ce da yawa daga cikin manyan kwamandojin ƙungiyar sun mutu ne sakamakon rikicin shugabanci da ya ɓarke tsakanin mayaƙan ƙungiyar ISWAP da mayaƙan Boko Haram masu biyayya ga marigayi Abubakar Shekau bayan ya rasu a shekarar 2021.

Ya ce: “Ɗaya daga cikin shugabannin su ya ce a cikin 300 daga cikin su da suka fara ƙungiyar Boko Haram tun kafin shekarar 2009, mutane ƙasa da 10 ne suke raye a yanzu. Hatta sauran shugabanni goma da suka rage sun watse saboda rikici kan shugabancin ƙungiyar.

“Wasu sun mutu sakamakon saran macizai a daji, wasu sun mutu sakamakon harin sojoji, wasu sun nutse a ruwa lokacin damina, wasu sun mutu sakamakon harbin bindiga; wasu a sakamakon gagarumin miƙa wuya da muka shaida a cikin shekaru biyu da suka wuce.

“Wasu sakamakon faɗan da ake yi a tsakanin su saboda muƙaman shugabanci, musamman bayan rasuwar Shekau wanda hakan ya janyo mutuwar sama da kashi 90 cikin ɗari na waɗanda suka mutu da aƙidar Boko Haram.

“A ɗaya ɓangaren kuma, manyan kwamandojin ISWAP da dama sun rasa rayukan su sakamakon rikice-rikice da dama a tsakanin su.

“Don haka, idan kuka duba, aƙidar ta tafi kuma zan iya gaya maku cewa waɗanda ke nuna kan su a yanzu miyagu ne kawai waɗanda ba su da aƙidar.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?