Back

Kashim Shettima Zai Kaddamar Da Aikin Wutar Lantarki A Kudu Maso Yamma Ranar Litinin

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, zai kaddamar da shirin haskaka kudu maso yamma (Light Up South East Initiative.) a ranar Litinin mai zuwa, domin kara samar da wutar lantarki ga kungiyoyin da masana’antu a yankin.

An bayyana hakan ne a wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban kasa kan harkokin yada labarai da sadarwa, na ofishin mataimakin shugaban kasa Stanley Nkwocha ya fitar ranar Juma’a.

Taron wanda aka shirya gudanarwa a garin Enugu, babban birnin jihar Enugu, ci gaba ne da kokarin inganta samar da makamashi ga kungiyoyin masana’antu da gwamnatin Najeriya ke yi a fadin kasar nan.

Aikin, na hadin gwiwa tsakanin Kamfanin Neja Delta Power Holding Company Limited (NDPHC) da abokan huldar sa, zai kunshi manyan masu ruwa da tsaki a harkar wutar lantarkin kasar.

Wani muhimmin abin da mataimakin shugaban kasar zai gabatar a Enugu a ranar Litinin din shi ne taron kasuwanci na Kudu maso yamma wanda manyan jami’an gwamnati da shugabannin ‘yan kasuwa za su tattauna kan isar da ingantacciyar madogara mai dorewa ga masana’antu da wuraren zama a yankin.

A ranar sha biyu ga watan goma na shekarar da ta wuce, mataimakin shugaban kasar ya kaddamar da shirin a yankin Kudu maso Yamma a rukunin masana’antu na Agbara, tare da masu ruwa da tsaki wajen ganin an samu nasarar aiwatar da aikin a fadin kasar nan.

Tun daga farko gwamnatin Tinubu ta himmatu wajen sake fasalin tsarin samar da ababen more rayuwa na Najeriya tare da kokarin da ake bukata don karfafawa ‘yan Najeriya da karfafa manufofin tattalin arzikin kasa.

Hakazalika, a wannan rana mataimakin shugaban kasar zai kaddamar da aikin samar da wutar lantarki mai karfin megawatt dari da tamanin da daya a rukunin masana’antu na Osisioma, Aba, jihar Abia.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?