Ovie na Masarautar Ewu-Urhobo, ƙaramar hukumar Ughelli ta kudu a jihar Delta, Mai Martaba Sarkin, Clement Oghenerukevwe Ikolo, Urhukpe 1, ya miƙa kansa ga rundunar ‘yan sandan jihar.
Sarkin dai na ɗaya daga cikin mutane takwas da Hedikwatar Tsaro (DHQ) ta bayyana tana nema ruwa a jallo saboda rawar da suka taka da kuma alaƙa da kisan gillar da aka yi wa sojoji 17 a ƙauyen Okuama da ke masarautar Ewu-Urhobo ta ƙaramar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta.
,Ikolo ya miƙa kansa da yammacin Alhamis a ofishin ‘yan sandan jihar Delta da ke Asaba, kuma Kwamishinan ‘Yan Sandan, CP Abaniwonda Olufemi ya tarbe shi.
Sarkin dai ya kasance yana zaune ne a birnin Landan na ƙasar Birtaniya, kafin a zaɓe shi a matsayin Ovie na Masarautar Ewu-Urhobo.
Gwamnan jihar Delta Hon. Sheriff Oborevwori, ne ya bashi ragamar mulki a watan Nuwambar bara.
Blueprint ta tattaro cewa sarkin bai koma masarautarsa ba tun bayan bikin naɗin sarautar sa kan wata taƙaddamar doka da ta taso daga zaɓen da aka yi masa biyo bayan murabus dɗn tsohon sarkin.
Da yake yiwa ‘yan jarida bayani kafin ya miƙa kansa ga ‘yan sanda, Sarkin ya musanta cewa yana da hannu wajen kashe sojojin 17, waɗanda suka haɗa da manyan hafsoshi huɗu da sojoji 13 na bataliya ta 181 ta Amphibious na sojojin Nijeriya.
Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da na jihar Delta da su kafa wani kwamitin bincike mai zaman kansa domin gudanar da bincike kan kisan da aka yi wa jami’an soji a cikin al’ummar Okuama na masarautarsa.
HRM Ikolo ya ci gaba da cewa ya yanke shawarar gabatar da kansa ga hukuma domin tabbatar wa gwamnatin Nijeriya da ƙasashen duniya cewa ba shi da hannu ko alaƙa da waɗanda suka kashe sojojin.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na ‘Yan Sandan (PPRO), SP Bright Edafe, ya tabbatar da cewa sarkin ya miƙa kansa ga ‘yan sanda.
Okuama, al’ummar Urhobo, na ɗaya daga cikin al’ummomi sama da 40 da ke ƙarƙashin mulkin sarkin a masarautar Ewu-Urhobo.