Mai Shari’a Inyang Edem Ekwo na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, a ranar Litinin, ya yi watsi da buƙatar da mai sulhu da ‘yan ta’adda, Mohammed Tukur Mamu, ya yi na a ɗauke shi daga hannun Hukumar Tsaro ta farin Kaya (DSS), zuwa gidan yarin Kuje da ke Abuja.
Mamu dai yana fuskantar shari’a kan laifukan ta’addanci, kuma yana hannun DSS bayan da kotu ta ƙi bada belinsa.
Mai Shari’a Ekwo, yayin da yake yanke hukunci na baya-bayan nan, ya ce Gwamnatin Tarayya ta yi tsokaci kan batun fasa gidan yari a gidajen yari a matsayin babban dalilin ƙin amincewa da buƙatar sa ta kai shi Kuje.
Ya ci gaba da cewa, Mamu bai musanta zargin da aka yi masa ba kamar yadda doka ta tanada.
A cewar Mai Shari’ar, tunda Mamu bai ƙalubalanci zargin ba, ana ganin gaskiya ne kuma gaskiyar da aka shigar ba ta buƙatar ƙarin hujja.
Daga nan ya umarce shi da ya ci gaba da zama a hannun DSS a duk tsawon shari’ar da ake yi masa na laifukan da ake tuhumar sa.
Mai Shari’a Ekwo, ya tabbatar da umarnin da ya bayar tun farko cewa a bar ɗan ta’addan ya nemi likitansa domin magani ƙarƙashin kulawar hukumar DSS.
Mamu, ta bakin lauyansa, Abdul Mohammed, SAN, a ranar 29 ga watan Afrilu, ya yi zargin cewa DSS ba ta bi umarnin da kotu ta bayar a ranar 19 ga watan Disamba, 2023, na a ba shi damar zuwa wurin likitansa domin neman lafiya.
Ya yi iƙirarin cewa an ba shi damar ganawa da likitan sau ɗaya inda aka miƙa rahoton cikakken binciken lafiyarsa ga hukumar DSS.
Tun bayan gabatar da rahoton, Mamu ya yi zargin cewa ba a ba wa likitan damar isa gare shi ba, don haka yana buƙatar a yi masa tiyata cikin gaggawa a kowane asibiti a ƙasar.
Wanda ake tuhumar ya ci gaba da cewa tun daga lokacin ne lafiyarsa ta taɓarɓare kuma zai iya rasa ransa kowane lokaci idan ba a ɗauke shi daga hannun DSS zuwa gidan yarin Kuje ba.
Ya yi alƙawarin zuwa kotu akai-akai, inda ya ƙara da cewa zai iya tsayawa shari’a ne kawai idan yana raye.