Back

Kotu ta bada umarnin tsare makashin sarakunan Ekiti 2

Wata ƙaramar kotu a jihar Ekiti ta bayar da umarnin tsare ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi da yin garkuwa da wasu sarakunan gargajiya biyu a jihar.

Alƙalin kotun, O. F. Bamidele, ya bayar da umarnin tsare Bubuga Lede mai shekaru 25 a gidan yari na Ado-Ekiti na tsawon kwanaki 30 a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi da hannunsu wajen yin garkuwa da Oba David Babatunde Ogunsakin da Oba Samuel Olatunde Ishola.

Ɗan sanda mai shigar da ƙara, Insifekta Osuolale Yomi, wanda ya ce laifin yana da hukunci a ƙarƙashin sashe na 280, 241 da 234 na dokar laifuka ta jihar Ekiti 2021, ya ƙara da cewa an kama wanda ake tuhuma a Ikole-Ekiti a ranar 29 ga watan Janairu, da muggan makamai.

An ɗage sauraren ƙarar zuwa ranar 24 ga watan Afrilu domin sauraren ƙarar.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?