Back

Kotu ta bayar da belin Emefiele kan naira miliyan 300 kan wasu sabbin tuhume-tuhume

Mai Shari’a Maryanne Anenih na Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya da ke Maitama ta bayar da belin tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Godwin Emefiele, a kan kuɗi naira miliyan 300.

An bayar da belin ne bayan gurfanar da shi a gaban kotu kan tuhume-tuhume guda huɗu da ake masa na buga sabbin takardun naira ba tare da bin ƙa’ida ba.

Emefiele ya ƙi amsa laifin da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) take tuhumar sa dashi.

Sauran sharuɗɗan belin sun haɗa da cewa ya gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa waɗanda kowannensu ya mallaki kadara mai sunansa a yankin Maitama da ke Babban Birnin Tarayya (FCT).

Mai Shari’a Anenih ta umarci wanda ake ƙara da ya ajiye takardun tafiyarsa a gaban kotu kuma kada ya fita ƙasar waje ba tare da izinin kotu ba.

Ta ɗage zaman har zuwa ranar 28 ga watan Mayu domin fara shari’ar.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?