A ranar Juma’a ne wata Kotun Laifuka ta Musamman da ke Ikeja ta ba da belin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, (CBN), Godwin Emefiele, da aka dakatar, kan kuɗi naira miliyan 50.
Ana tuhumar sa da laifin amfani da ofishin sa ta hanyar da bata dace ba da kuma zambar dala biliyan 4.5 da kuma naira biliyan 2.8.
Mai Shari’a Rahman Oshodi, a hukuncin da ya yanke, ya amince da bayar da belin Emefiele tare da mutane biyu da za su tsaya masa.
Oshodi ya ce dole ne waɗanda za su tsaya masa suna da aikin yi sannan sun biya haraji na tsawon shekaru uku ga Gwamnatin Jihar Legas.
Ya kuma ba da umarnin cewa sai waɗanda za su tsaya musa sun nuna shaidar da ta dace kuma sai suna da rajista a Tsarin Kula da Beli na Jihar Legas.
Alƙalin ya kuma ce ya gamsu da sharuɗɗan belin naira miliyan 1, wanda tun da farko aka baiwa wanda ake tuhuman sa tare da Emefiele, Henry Isioma-Omoil, wanda aka gurfanar kan wani laifin a gaban Mai Shari’a Olufunke Sule-Hamzat a wata Babbar Kotun Yaba.
Sai dai Oshodi ya ce dole ne a miƙa takardun belin ga kotun laifuka ta musamman sannan kuma a yi rajista a Tsarin Kula da Beli na Jihar Legas.